1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaLaberiya

Laberiya. Shaye-shayen mataasa ya yawaita

October 31, 2024

Hukumomin lafiya a kasar Laberiya na cikin zullumi da fargaba, kan yadda za su tunkari matsalar shaye-shayen muggan kwayoyi a tsakanin matasa.

Laberiya | Kush | Matasa
Yadda matsa ke kassara rayuwarsu a Laberiya, ta hanyar shan wiwi mai suna "Kush"Hoto: Christian Dransfeld/DW

Gwamnatin Laberiya na cikin wadi na tsaka mai wuya sakamakon rasa galibin matasan da ke kasancewa alkiblar kasar ta hanyar shan miyagun kwayoyi musamman "Kush", guda daga cikin nau'in tabar wiwi da ke jirtaka kwakwalwa ko kuma haukatar da dan Adam da aka fi sani da K2 ko kuma Spice a sauran kasashen duniya. A 'yan shekarun baya-bayan nan cutar ta yi wa matasan Laberiya illa, wasu sun haukace wasu sun rasa kafafu da sauran gabobinsu kai wasu ma sun riga mu gidan gaskiya. Kwayar "Kush" na ci gaba da raraka cikin gaggawa a tsakanin matasan Monrovia babban birnin kasar ta Laberiya, inda kwararru kamar likita a asibitin masu fama da lalurar kwakwalwa Dakta Emmanuel Flomo ke cewa sai gwamnati ta tashi tsaye wajen ceto wadannan matasa daga halaka.

Magance zaman kashe wando a Laberiya

03:18

This browser does not support the video element.

Wakiliyar DW da ke birnin Monrovia Evelyn Kpadeh ta yi shigar burtu cikin matasan da ke da rangwamen hankali a birnin, inda ta tattara mana alkaluman abin da ta gani a mashayar matasa da ke cike da tashin hankali. Ta iske wasu matasan ba sa iya zama sai a tsaye suke bacci, wasu kuma ba sa iya kwanciya saboda hannaye da kafafunsu a mimmike suke ba za su iya lankwasa gabobinsu ba. To da yake lamarin shaye-shayen miyagun kwayoyi ya zama gobara daga kogi a nahiyar Afirka, wani mai tabin hankali a kasar Afirka ta Kudu kuma tubabben dan bindiga ya ce nau'in tabar wiwin mai matukar hadari wato "Kush" ya haukata matasa da dama tare da jefa su cikin kogin nadama.