1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda a bisa shugabancin Al-Sisi

Mahmud Yaya AzareJune 6, 2015

A yayin da ake cika shekara guda da hawan shugaba kasar ta Masar kan mulki, yan kasar na ci gaba da korafi kan rashin ganin wani sauyi a kasa, hasalima sai yin suka kan kazantar keta hakkin jama'a

Ägypten Ansprache Präsident al-Sisi in Kairo 25.10.2014
Hoto: Reuters/The Egyptian Presidency

Sabanin shekarar farko ta hambararren shugaba Muhammad Mursi, wacce kafofin watsa labarai da masharhanta suka yi ta fashin baki kanta, shekarar farko ta shugaban Sisi, ta zo ta wuce salim-alim, ba tare da kafofin watsa labarai sun dorata akan mizani ba. Hakan kuwa a ta bakin magoya bayan Sisi, bai rasa nasaba da halin yaki da ta'addanci da kasar ta Masar ta samu kanta ciki ba.
"Ya yi matukar kyau da muka sami kanmu haka a yanzu. Duk da yakin da muke fafatawa da 'yan ta,adda, an yi man'yan ayyukan raya kasa a wannan shekarar, da suka hada da gina mashigin ruwa na Suez da gadoji da hanyoyi, gami da karin albashin ma'aikata. An magance cunkoso kan tituna"

Wasu kuwa, yabawa Sisi din suke, kana abin da suke ganin hana fadawa kasar cikin yakin basasa da ya yi. "Wallahi kadan muka ga abin da ke faruwa a makwabtanmu irinsu Siriya da Iraki da Libiya, ba abin da zamu yi sai godiya ga wannan gwarzon da ya tabbatar mana tsaro a kasarmu. Kan banda yakar ta'addanci da yake ci-gaba da yi. Allah dai ya kare shi"

Hoto: AFP/Getty Images


Shawo kan matsalar yakin basasa ce koma ta tsaro, Sisis din ya yi nasarar kawarwa a kasar ta Masar, amma wasu 'yan kasar kuwa, a hannu gudu akasin hakan suke gani; "Ta'addanci kan shi ne abin da jami'an tsaro ke yi, na kakkashe masu zanga-zanga. Da kuma hukunce-hukuncen da alkalai ke yankewa na hukuncin kisa barkatai. Da kuma watsi da ake da masu jinya a asibitotci har su mutu. Wannan shi ne tsagwaron ta'addanci, kadanma har akwai shi a Masar"


A shekara gudar da Sisis din ya yi kan karagar mulki, ya sanya dokoki da dama da suka shafi inganta aikin gwamnati da hana lalata kayyakin gwamnati. Kan banda hana masu tallace-tallace da kasa kayayyaki kan tituna, dama dokar hana zanga-zanga sai da izini. Dokar da masu rajin kare hakkin jama'a suka ce, taci karo da kundin tsarin mulkin kasar.

Hoto: picture-alliance/dpa/Elfiqi


"Ya yi matukar sabawa hankali a ce, don dan kasa ya fita ya yi zanga-zanga, kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba shi dama, a ce za'a kama shi a amar daurin shekaru biyar, ko jami'an tsaro su jikkata shi koma su kashe shi"
Su kuwa masu rayuwar hanu baka hanu kwarya, wadanda shugaba Sisi din ya yi ta barar kudade daga wajen sarakunan Larabawa da sunan kyautata rayuwarsu, cewa suke gwara jiya da yau.


"Farashi ya yi tashin gwauran zabi. An janye tallafi daga makamashi da kayakin masarufi. Wutar lantarki bata zama. Ga karancin man fetur a gidajen mai"
Suma Kungiyoyin kare hakkin jama'a cewa suke, shekara guda bayan da Sisi ya dare kan karagar mulki, fursunonin siyasa da suka dara dubu 40 a kasar, sun sake shiga cikin mawuyacin hali, yadda ake zargin gana wa wasunsu azaba da hana danginsu ziyarartarsu. Lokotun da doka ta tanada, gami da rasuwar sama da fursunoni 160 a cikin gidajen yari, sakamakon rashin kai su asibiti kan lokaci.