1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da boren neman sauyi a Siriya

March 15, 2012

Har yanzu ba'a samu mafita ga rikicin Siriya ba duk da cewar shekara ɗaya kenan da yunƙurin neman bin tafarkin dimoƙraɗiyya.

Syrian protesters chant anti-Bashar Assad slogans under a large revolutionary flag during a protest in front the Syrian embassy in Amman, Jordan, Friday, March 9, 2012. Hundreds of Syrians attend the Friday prayer, prior to a protest in front the Syrian embassy to demand International intervention and to arm the Free Syrian Army. (AP photo/Mohammad Hannon)
Hoto: AP

A wannan Alhamis ce Siriya ke cika shekara ɗaya da fara rigingimun neman kawar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na ƙasar, koƙarin da kuma ya zuwa yanzu ba'a kai ga samun hanyar diflomasiyyar warware shiba. A yayin da ake ci gaba da yin fito-na-fito a tsakanin dakarun gwamnatin Siriya da 'yan adawar ƙasar, a yanzu ƙasar Rasha ta bi sahun manzo na musamman da ƙasashen Larabawa da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya suka naɗa domin shiga-tsakani a rikicin na Siriya wato Kofi Annan, wajen yin ƙira ga shugaba Assad daya hanzarta aiwatar da sauye sauyen da za su kawo ƙarshen rikicin da ƙasar ke fama da shi.

A wannan Jumma'ar ce kuma Mr Kofi Annan ke yiwa kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya jawabi game da martanin da hukumomin na Siriya suka mayar ga jerin shawarwarin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gabatar da nufin kawo ƙarshen rigingimun. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewar mutane dubu takwas ne - galibin su fararen hula suka mutu a lokacin tashe-tashen hankulan dake cika shekara guda kenan a wannan Alhamis.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman