1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da fara bore a Siriya

March 15, 2012

Rigingimu na neman sauyi zuwa tafarkin democraɗiyya a Ƙasashen larabawa, na ci gaba da haddasa asarar rayuka a Siriyar, bayan irin nasarori da wasu su cimma.

Supporters of Syria's President Bashar al-Assad attend a rally at Umayyad square in Damascus March 15, 2012. REUTERS/Khaled al-Hariri (SYRIA - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Shekara guda kenan da 'yan adawa a kasar siriya suka kaddamar da zanga-zangar bukatar hamɓarar da gwamnatin ShugabaBashar al-assad. Waɗannan rigingimu na neman sauyi zuwa tafarkin democradiyya a ƙasashen larabawan dai sun somo ne daga Tunisiya da Masar da Libya kafin ya isa Siriyar. Rikicin na Siriya dake ci gaba da ɗaukar hankalin Duniya dai, yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

Zanga-zangar Ɗalibai a birnin Damuskus fadar gwamnatin Syriya, a ranar 15 ga watan marisn na shekara ta 2011 data gabata. Wannan shine ranar farko da kaddamar da wannan rikici na neman kifar da gwamnatin shugaba Bashar al-assad daya ki ci yaki cinyewa.

Assad yace " babu batun sasantawa da 'yan ta'adda, waɗanda ke dauke da makamai domin haifar da rigingimu, kazalika babu maganar daidaitawa da wadanda ke haɗa baki da ƙasashen ketare domin hambarara da mu".

Hoto: AP

Wa shugaban na Siriya dai Ɗaliban sune 'yan ta'adda, sakamakon gangamin da suka yi a bara na nuna adaw da gwamnatinsa tare da bayyana gwamnatinsa da munanan kalamai. wannan adawa da gwamnatin Assad dai ya jagoranci kame Ɗaliban, Iyayensu sun bukaci a sako su, ammam gwamnati tayi watsi da hakan, wanda shine ya zame ummul aba'isin halin da Siriya ta tsinci kanta a ciki a yau na boren adawa.

Irin munana kalaman masu boren Siriyan kenan na bukatar hambarar da gwamnatin Assad, wanda ya jagoranci cafke mutane da dama a ɓangaren jami'an tsaro. Batu kuma da masu adawn ke ganin take 'yancin walwala da faɗin albarkacin bakin al'umar kara ne. Kamar yadda manazarci kan lamuran Damasus Thabet Salem ya nunar...

" Yace idan har aka bar mutane su faɗi albarkacin bakinsu, ina ganin ba zai samu rinjayen magoya baya , musamman bayan abubuwanda suka faru. Ko da yake hakan na bukatar bincike , da jin ra'ayoyin jama'a. Amma a nawa ganin Assad yana da kashi 30 zuwa 35 daga cikin 100 kachal nena yawan magoya ba"

Acewar shugaba Bashar al-Assad dai gyare gyaren da gwamnatinsa ke yi nada fuskoki biyu...da suka kunshi siyasa da yaƙar ayyukan ta'addanci.

An dai dauki tsawon lokaci na ƙoƙarin gano bakin zaren warware rikicin na Syria amma lamarin yaci tura. Inda har ya zuwa wannan lokaci sojojin gwamnati na cigaba yin arangama da masu boren adawa a mayan biranen kasar da suka hadar da Homs.

Hoto: AP

Hausawa dai kance gani ga wane ya isa wane tsoron Allah, kasancewar ba Siriyar ce kadai aka fara gudanar da irin wannan bore ba, a kasashe kamar Tunisiya, Masar da Libiya an cimma nasara, wasu na ganin kamata yayi shugaba Assad ya amsawa bukatun 'yan adawan kasar. Tare da tafiya gudun hijira kamar na shugaban kama karya Saleh na Yemen. Duk da cewar yaya Syriya zata kasance ba tare da Assad da mukkarrabansa wadanda sune masu hannu da shunin kasar ba? sai dai yin gudun hijira itace mafi a'ala a garesu, domin kare karuwar asarar rayuka da ke ci gaba da fuskanta, kamar yadda Hilal Khashan na jami'ar Amirka dake birnin Beirut ya nunar...

" Ina ganin cewar Siriya ba zata samu zaman lafiya nan da shekara guda ba. Sai dai kafin wannan lokaci Assad ya riga ya ya fice".

Wa 'yan Adawar ƙasar, wanda ke ganin gwamnatin Assad a matsayin ta kama karya mai kisan gillar al'umma, wannan bore zai cigaba har sai sunga abunda ya ture wa buzu naɗi.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal