Shekara guda da harin birnin Nice
July 14, 2017Talla
A ranar 14 ga watan Yulin bara ne dai wani mahari mai suna Mohamed Bouhlel ya kutsa da wata babbar mota a tsakiyar jama'a inda a cikin mintuna kalilan aka samu asarar rayukan mutane 86 ciki har da kananan yara. Shugaba Emmanuel Macron ya jagoranci sauran al'ummar kasar a taron da aka yi don gudanar da addu'oi da kuma karrama wadanda suka nuna bajinta a lokacin harin.
Daga cikin mutane fiye da dari hudu da suka sami rauni sakamakon harin na birnin Nice, har ya zuwa wannan lokacin akwai wasu da ke gadon asibiti suna jiyar munanan raunin da suka samu. Bincike ya nuna cewa Maharin mai suna Mohammed Bouhlel dan kasar Tunisiya ne da ke da izinin zama a Faransar.
Mahukuntan Faransa na ci gaba da tsare wasu mutane tara da ake zargi da hannu a harin.