1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko Afirka ta tasirantu da juyin-juy hali?

December 17, 2020

Shekaru 10 ke nan da wani dan kasar Tunisiya ya kashe kansa domin nuna adawa da cin zarafin da hukumomin tsaro ke yi, abin da ya janyo juyin-juya halin da ya yi awon gaba da kujerun wasu shugabannin kasashen Larabawa.

Symbolbild Arabischer Frühling Tunesien
Masu zanga-zanga a Tunusiya dauke da babban hoton Mohamed Bouazizi da ya kashe kansaHoto: picture-alliance/AP Photo/Salah Habibi

Shekaru 10 ke nan da Mohamed Bouazizi dan Tunusiya ya kona kansa a garin Sidi Bouzid bayan da jami'an tsaro suka ci zarafinsa. Abin da ya janyo zanga-zanga da bore a ilahirin kasashen Larabawa. Da farko boren ya yi awon gaba da kujerar mulkin shugaban Tunisiyan Zine el-Abidine Ben Ali. Sai kuma shugaban Masar Hosni Mubarak da shugaban Yemen Ali Abdullah Salih da kuma Mu'ammar Gaddafi na Libiya suka biyo baya.

Karin Bayani: Halin rashin tabbas a Tunusiya

Sai dai shekaru 10 bayan kadawar guduwar canji, fatan samun wani sauyi na a zo a gani bai tabbata ba. Domin har yanzu gwamnatocin mulkin kama karya da yake-yaken basasa da ayyukan masu ikirarin jihadi, sun zama ruwan dare a wasu kasashe.

Amma duk da haka boren na kasashen Larabawa ya karfafa gwiwa a wasu kasashen duniya ciki har da na Afirka, koda ya ke ba a ga irin wannan bore a kasashen Afirkan ba, duk kuwa da cewa matsalolinsu kusan iri daya ne da na kasashen Larabawan. Misali a 2014 dubun-dubatar mutane a Burkina Faso sun gudanar da zanga-zangar adawa da neman karin wa'adin mulkin Shugaba Blaise Compaoré da a lokacin ya kwashe shekaru 27 kan mulki. A Senegal a 2012, wata kungiyar matasa ta yi nasarar juya hukuncin kotun tsarin mulki da ta sahalewa Shugaba Abdoulaye Wade damar neman wa'adin mulki karo na uku. Sannan a Sudan zanga zanga a 2019, ta kawo karshen mulin Shugaba Omar al-Bashir. Robert Kappel masanin kimiyyar siyasar Afirka ya ce ko shakka babu borin na kasashen Larbawa ya zama abin koyi a Afirka: "A gani-na abubuwan da suka faru a yankin arewacin Afirka da na Gabas ta Tsakiya, sun karfafa gwiwar kungiyoyin fafutukar neman mulkin dimukuradiyya da 'yancin walwala da na fadin albarkacin baki da kare 'yancin dan Adam a Afirka."
Sai dai Matthias Basedu daraktan cibiyar nazarin harkokin Afirka ta GIGA ya ce ba a ga bore na gama gari a Afirka ba, domin tun bayan karshen yakin cacar baka a mafi yawan kasashen Afirkan, an kawar da shugabanni na sai Mahadi ya bayyana, saboda hakazanga-zangar da aka samu a Burkina Faso da Senegal da Sudan sun dan bambanta.

Zanga-zanga a Burkina FasoHoto: Reuters/J. Penney

Karin Bayani: Sharhi kan rikicin kasar Sudan

Gilbert Achcar farfesa na huldodi tsakanin kasa da kasa a jami'ar SOAS da ke birnin London na kasar Birtaniya, ya ce bambancin matsalolin kasashenLarabawa da na Afirka na daga cikin dalilan da suka hana samun irin borin Larabawa a yankin Kudu da Saharar Afirka. Duk da haka boren ya yi mummunan tasiri a wasu kasashen Afirka misali yankin Sahel, inda bayan kifar da shugaba Muammar Gaddafi a Libiya yankin ya kara tsunduma cikin rikici musamman ma arewacin Mali.