1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shekaru 100 da kafuwar jam'iyyar Kwaminisanci a China

Suleiman Babayo MA
July 1, 2021

Jam'iyyar Kwaminisanci mai mulkin kasar China ta cika shekara 100 da kafuwa a wannan mako, inda Alhamis daya ga watan Yuli ta cika shekarun. Ta kuma kwashe shekaru 72 tana mulki.

China 100. Jahrestag der Kommunistischen Partei
Hoto: Ng Han Guan/AP/dpa/picture alliance

Jam'iyyar Kwaminisancin na da mambobi miliyan 90 a daukacin fadin kasar kuma tana kara karfi fiye da kowane lokaci. Domin ci gaba da mulkin kasar ta China jam'iyyar ta dauki matakai daban-daban. Mambobin jam'iyyar ta kwaminisanci kan yi rantsuwa mubayi'a. Tun daga kan manyan jam'iyyar Shugaba Xi Jinping da wasu jiga-jigan jam'iyyar 50 sun yi irin wannan rantsuwa a tsakiyar watan Yuni, a gidan ajiye kayan tarihi da ke birnin Beijing fadar gwamnatin kasar ta China.

Hoto: Ng Han Guan/AP/picture alliance

Gwamnati ta yada wannan mubayi'ar kai tsaye ta kafofin yada labarai na kasar. Haka ma ta karfafa matakan farfaganda na jam'iyyar ko a matakin China ya wuce abin da aka saba gani. A duk fadin China an kafa tutocin jam'iyyar mai mulki albarkacin cika shdekaru 100 da kafuwa.

 

Tashoshin talabijin da rediyo gami da shafukan intanet na cike da bayanan irin nasarar da mulkin jam'iyya daya ya haifar. An samu sauye-sauye da dama kuma Shugaba Xi Jinping ya kawar da tsarin da ya kayyade wa'adi biyu na mulkin shekaru biyar-biyar, inda bayan shekara 10 ake samun sabon shugaba.

Hoto: Li Xueren/XinHua/dpa/picture alliance

Jam'iyyar kwaminisanci mai mulkin China ta ce tana da mambobi milyan 91. Mambobin ke tafiyar da hukumomin gwamnati amma wani lokaci har da kamfanoni masu zaman kansu. Amma wadanda suke da gaskiya da amana da iya tafiyar da harkoki babu rashin gaskiya ake zaba cikin wannan tsari.

 

Ya kan dauki shekaru kafin mutum ya zama cikakken memba. Wani da yanzu haka yake cikin wannan tsarin neman zama mamba shi ne Gao Cong dan shekaru 29 da haihuwa a garin Xi'an na tsakiyar China.

Ana samun masu sukar jam'iyyar kwaminisanci a China, amma ba a fili ba. Saboda tsoron rasa aiki ko hukunci. Jam'iyyar Kwaminisanci mai mulkin China kullum tana bayar da amsa kan mulkin kama karya na jam'iyya daya