Nijar: Rashin aiwatar da hukuncin kisa
April 9, 2019Tun bayan da kasar ta samu 'yancin cin gashin kanta a 1960, Nijar ta fuskanci juyi da yunkurin juyin mulki kai dai dai har sau shida. Kama daga na Seyni Kountche da Sani Sounna Siddo da Moussa Bayer da na Amadou Umar Banko ya zuwa na Bare Mainassara da na baya-bayan nan na Janar Salou Jibo da ma lugudan wutar da wani jirgin saman sojoji yayi a wani kauyen yankin Diffa. Inda ko shakka babu an samu asarar rayuka da dama.
To amma ya zuwa yau babu wani hukuncin da aka dauka a kan wadanda ke da hannu a kisan, abunda ya kai kungiyoyin farar fula masu rajin kare hakin bil Adama nuna damuwarsu a dangane da kunnen uwar shegu da gwamnatoci ke yi a kasar a dangane da batu, hakan dai na zaman wani kalubale ga demukradiyyar Nijar.
To ko baya ga kaurin sunan da kasar tayi wajen juyin milki, dalibban kasar da dama ne suka kwanta damarsu a yayin gwagwarmayar da suke yi ba tare da an hukunta masu hannu a kisan nasu ba, abunda ya ba kungiyar dalibban kasar ta USN damar bukatar ganin an soke ayar dokar da ke yiwa masu laifufuka afuwa a kundin tsarin milkin kasar.
Masu nazarin lamura na ganin sannu a hankali rashin hukunci a kasar ya fara samun gurbin zama a kasar, lamarin da suke dangantawa da siyasa. An dai sha kai ruwa rana tsakanin iyalan wadanda aka hallaka da hukumomin kasar ba tare da an cimma nasara ba.