1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 20 bayan sako Mandela daga gidan Yari.

February 11, 2010

Alúmar Afrika ta kudu na bikin cika shekaru 20 bayan sakin Mandela daga gidan Yari.

Shugaban Jamíyar ANC Nelson Mandela ke jawabi jim kadan bayan fitowarsa daga gidan yar a ranar 11 ga watan Fabrairu 1990.Hoto: picture-alliance / dpa

A ranar 11 ga watan Fabrairu na shekarar 1990 aka sako, gwarzon Afirka ta Kudu Nelson Mandela daga gidan yari. Shekaru huɗu bayan haka, Mandela ya samu ɗarewa shugabancin ƙasar. Duk da cewa yanzu shekaru 16 bayan zaɓensa a matsayin shugaban ƙasa baƙar fata na farko a ƙasar, amma har yanzu ‘yan ƙasar suna bashi daraja sosai.

A yammacin ranar da aka sako Mandela mutane kimanin dubu hamsin suka yi cincirindo a tsakiyar birnin Cape-Town. Waɗansu na tafiya a ƙafa wassu na kan saman barandar gidajen sama, dai dai sauransu. A wannan lokacin mahukunta a gwamantin shugaba F.W. de klerk sun yi tsammanin samun kawo sauyi, da sasantawa a guguwar siyasar ƙasar, amma ina, batun adawa da mulkin wariyar jinsi sai ma ƙaruwa yake samu daga Mandela. Don haka mahukuntan a wancan lokacin suka farayin da na shina.   

Yanzu shehkaru 20 bayan kawo ƙarshen mulkin wariyar jinsi, kundin tsarin mulkin ƙasar Afirka ta kudu, yana ɗaya daga wanda ake misali dashi wajen bawai kowa yancinsa a duniyar nan.

Ko dayake har yanzu akwai batun cin hanci da rashawa dama masu aikata manyan laifuka, amma dai masu lura da yadda ƙasar ke tafiyar da al'amuranta na ganin cewa Afrika ta Kudu ta samu gagarumin sauyi na cigaba. Wolfgan Derechsler wani ɗan jaridane da yayi shekaru 25 a matsayin waklin jaridar Handleblattes tanan Jamus daga Afirka ta Kudu.

“A da wata ƙasace da tayi fice wajen kisan mutane ba gaira ba dalili, ƙasace da aksarin al'ummarta basu da yanci, amma yanzu idan mutun ya tuna baya, to dole yace lamari ya canza a ƙasar Afirka ta kudu. Akwai matsaloli da yawa har yanzu, kamar yadda yake a zahiri. Amma dai  zamu iya cewa ƙasace mai bin tafarkin dimokraɗiya, inda miliyoyin mutane rayuwarsu ta samu ingantuwa”

Drechsler ya bayyana cewa dolene a jinjinawa rawar da Nelson Mandela ya taka, wajen kawo sauyi ƙasar.

Nelson Mandela ke jinjina ga dubban magoya bayansa.Hoto: AP

“A yanzu dai muna zuba idanu mu ga irin sauyin da za'a samu. Musamman irin matsalolin da jam'iyar ANC ke fama da su. Jami'iyar da akasarin jami'anta, mutane da da aka tsare su lokacin mulkin wariya jinsi. Ƙasar da a yanzu cin hanci yayi mata katutu. Ga matsalar kare gwamnatin Zimbabwe da sukeyi, ga cutar AIDS, waɗanan matsalolin duka, a ƙarƙashin mulkin Nelson Mandela suka faru”

Izuwa yanzu dai sambarka, domin ƙasar ta samu saukowa ƙasa daga matsayin da take, na ƙasashen da ake bin bashi, ƙasar tana murmurewa sannu a hankali. Kamar yadda Fikile Moya, Babban editan jaridar SOWETO, wadda ta taka mahimmiyar rawa, wajen ɗaukaka yaren baƙaƙen fatar ƙasar, lokacin yaƙi da mulkin wariyar jinsi.                                                      

"Abun kaicho shine, yanzu bamu da ci gaban da muke da shi shekaru 20 da suka gabata. Ko ma irin ratar dake tsakanin baƙaƙe masu hali da talakawa, izuwa yanzu ɗan ƙaramin canji muka gani. Aksarin yan ƙasar Afirka ta kudu, da a zamanin mulkin wariya, aka keɓesu, har yanzu batun haka yake. Cuɗanyar da Mandela ya yi yaƙi domin same ta tsakanin yan ƙasar, har yanzu babu abinda ya sauya”

Duk da waɗanan matsaloli dai ana kwatanta ƙasar Afirka ta kudu a matsayin ƙasar da tafi baiwa ƙungiyoyi masu zaman kansu yacin walwala a nahiyar Afirka. Inda kuma kowa yake da yancin gudanar da addininsa.

Mawallafa :- Schadomsky Ludger / Usman Shehu

Edita : Abdullahi Tanko Bala