Shekaru 20 da kisan kiyashi a Ruwanda
April 7, 2014Shekaru 20 bayan kisan kiyashin na Ruwanda, mutane kamar su François Kabagema da a yanzu haka yake da kimanin shekaru 45 a duniya na bayyana yadda suka shaidawa idanunsu yadda aka rika kashe mutane a yakin. Shi dai François Kabagema direban Taxi ne a Kigali babban birnin kasar Ruwandan kuma ya kwashe tsahon mako guda a ofishin jakadancin kasar Faransa dake Kigalin domin tsira da rayuwarsa a yayin da 'yan kabilar Hutu dake da rinjaye suke farautar 'yan kabilar Tutsi tsiraru. Daga cikin abun da François Kabagema ke iya tunawa a wani tsauni inda ya kasance gidansa a baya shine wasu bishiyoyi guda biyu da ya shuka tun yana karaminsa da a yanzu babu su.
Ya ce: " Nan ne gidan na. Da ba haka ya ke ba. Ina iya ganin bishiyoyi guda biyu da na shuka tun ina yaro. Duk yanzu basa nan suna da yawa ina ma da dan karamin lambu da kuma gidan gona".
Kabagema dai ya faro da ba da tarihin yakin ne tun daga ranar 22 ga watan Fabarairun shekara ta 1994 makwanni shida gabanin fara yakin kisan kiyashin da aka yiwa 'yan kabiyalr Tutsi. Tsahon wata guda suka kwashe suna shirya yadda za su yi kisan kiyashin. 'Yan kabilar Hutu masu rinjaye sun farma 'yan kabilar Tutsi tsiraru a kokarin da suke na shafe babinsu a doron kasa. Sun kuma kai a Gikundo inda Kabagema ke da zama shi kadai.
Tsallake rijiya da baya
"Cikin dare suka kai min hari. Sun jefa gurneti suka kuma yi harbi da harsasai a cikin gidana, sun ruguza gidan sai da suka tabbatar ba zan iya fitowa ba daga nan sai suka tafi sun dauka na mutu da kyar na sha".
Kabagema ya kara da cewa ya na zaune cikin fargabar yadda zai yi ya nemi mafaka a ofishin jakadancin Faransa. Wani ma'aikacin ba da taimakon raya kasa na kasar Faransa a wani gidan shakatawa kusa da inda Kabagem ke boye yana jin numfarfashinsa cikin dare da rana shine ya dauko shi domin ya bashi kariya. Ya ce cikin kwanaki hudu an kammala kwashe baki 'yan kasashen ketare dake birnin Kigali ofishin jakadancin faransa ma ya kwashe ma'aikatansa dake gidan shakatawar da Kabagema ke da zama inda shima ya shiga mota tare da su, sai dai kash bai samu damar tsira tare da su ba domin kuwa ya ce.....
"Ana haka sai wasu sojoji hudu suka zo a mota suka tambayeni kai waye? Kai Bafaranshe ne ko kuma dan Ruwanda? Ka amsa mana ko kuma mu kashe ka. Bani da zabi dole na fada musu ni dan Ruwanda ne daga nan sai suka fito dani daga motar suka cillar dani waje suka kuma shiga motarsu suka tafi.
Tsira bayan yanke kauna
Kabagema ya kwashe sama da tsahon wata guda a wanni gida yana cikin fargaba sai dai wanda ke kula da gidan ya taimaka masa matuka inda ya roki wani soja ya zo ya ganshi ya kuma bar masa makullan gidan kafin daga bisani ya dauke shi ya kashi ofishin jakadancin Faransa a ranar 19 ga watan Mayun shekara ta 1994 din. Kabagema ya kasance cikinn fargaba ko wane sakan guda yana tunanin shima za a zo a kashe shi kamar yadda aka kashe sauran 'yan uwansa.
A ranar hudu ga watan Yuli na shekara ta 1994 din ne aka samu nasarar shawo kan kisan kiyashin. Kabagema ya ce a yanzu al'amura sun fara dawo masa dai dai ya nemi aiki kuma ya mayar da hankalinsa kan kula da iyalansa. Ya ce ramuwar gayya bata da dadi in har ka kashe wani to kaima za a kashe iyalanka a dangane da haka ramuwar gayya bata taba kawo mafita.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu