Shekaru 25 bayan harin 11 ga watan Satumba na 2001, kungiyar Al-Qaeda ta rage karfi a duniya. Sai dai rassanta na da karfi a Afirka da Asiya da dabarunsu shi ne, na samun gindin zama a cikin gida.
Shekaru 25 da mummunan harin da aka kai kan cibiyar kasuwancin duniya a AmurkaHoto: dpa/picture alliance
Talla
Shekaru 25 da harin na 11 ga Satumba, Al-Qaeda ba ta kau ba kuma ba ta zama kungiya daya ba kamar yadda take da karfi a baya. Kungiyar ta yi rauni sossai, yayin da rassanta na yanki ke ci gaba da karfi a sassan Afirka da Asiya. Shalkwatar kungiyar da rassanta, sun zama marasa tsari. Farfesa Rüdiger Lohlker masani a fannin nazarin Musulunci ya ce, ta'addanci na kunshe da abubuwa da dama da ke zaman nakasu ga tattalin arziki da dole Turai sai ta kara azzama. A cewarsa, har yanzu da sauran aiki duk da karfin kungiyat ya ragu. Al-Qaeda ta rauni sossai, saboda nasarar da aka samu wajen yaki da ta'addanci bayan shekara ta 2001.
An karya lagon kungiyar?
Bincike a kan sha'anin ta'addanci ya nuna cewa, ayyukan sojoji a Afghanistan da kuma hadin gwiwa tsakanin hukumomin leken asiri da 'yan sanda. Sun karya lagon kungiyar, ta hanyar kifar da gwamnatoci masu alaka da ta'addanci. Kimanin shekaru 10 bayan hare-haren da aka kai a New York da Washington D.C., an kashe fitaccen jagoran al-Qaeda Osama bin Laden a watan Mayun 2011. Kisan nasa, ya zama abin da ya kasance babbar nasara. Sakamakon haka, Al-Qaeda ta sake tsara kanta. 'Yan ta'addar na neman wuraren da za su iya samun gindin zama na din-din-din, misali a sassan Afirka ko kuma a Yemen da sauran kasashe da ke da rauni.
Ranar 11 ga Satumban 2026 ne aka cika shekaru 25 da hare-haren ta'addanci a Amurka. Hotunan da aka dauka a ranar sun nuna firgici da barnar da hare-haren suka haifar, tare da zama muhimmin tarihin wannan rana.
Hoto: Henny Ray Abrams/AFP
Jirgin farko ya kutsa cikin Hasumiyar Arewa
A ranar 11 ga Satumban 2001, da karfe 8:46 na safe agogon Amurka, wani jirgi kirar Boeing 767 ya kutsa cikin babban benen Arewa ta cibiyar kasuwanci ta duniya WTC mai tsayin mita 417. Dukan mutum 92 da ke jirgin sun mutu. Hayaki ya turnuke saman ginin tare da haifar da rudani, yayin da kusan babu wanda ya fahimci cewa wannan ne farkon wani gagarumin harin ta'addanci.
Hoto: David Karp/AP Photo/picture alliance
An dauki hoton hari na biyu
Gidan talabijin na CNN ya fara nuna hotunan kai tsaye. Da karfe 9:03 na safe, duniya ta kalli yadda jirgi na biyu ya kutsa cikin benen Kudu ta WTC. Jirgin na dauke da mutum 65, wadanda duk suka mutu, yayin da sama da mutum dubu biyu suka rasa rayukansu a ciki da kewayen cibiyar kasuwancin duniya ta WTC.
Hoto: WABC television/CNN/dpa/picture alliance
Girman barnar harin ya fara bayyana
Wani bakin hayaki da wuta ya turnuke sararin Manhattan. Kimanin kashi biyu bisa uku na ginshikan da ke rike da benen Kudu sun lalace ko suka samu mummunar barna. A wannan lokaci ne aka fahimci cewa harin ta'addanci ne. An fara zargin cewa 'yan ta'adda ne suka sace jiragen, zargin da aka tabbatar jim kadan bayan haka.
Hoto: akg-images GmbH/epd
Labarin harin ya isa ga shugaban Amurka a Florida
A daidai wannan lokaci, shugaban Amurka George W. Bush yana ziyartar wata makaranta a Florida. Shugaban ma'aikatansa Andrew Card ya rada masa cewa jirgi na biyu ya kutsa cikin cibiyar kasuwanci ta duniya, kuma ana kai wa Amurka hari. Shugaba Bush ya nuna damuwa, amma ya ci gaba da zama yana sauraron daliban. Daga bisani ya bayyana cewa alamu na nuna cewa harin ta'addanci ne aka kai wa Amurka.
Hoto: Doug Mills/AP Photo/picture alliance
Harin da aka kai wa ma'aikatar tsaron Amurka watau Pentagon
Cibiyar kasuwanci ta duniya ba ita kadai aka kai wa hari ba. Da karfe 9:37 na safe, wani jirgin da aka sace ya kutsa cikin ginin ma'aikatar tsaro ta Pentagon da ke Washington. Jirgin Boeing 757 na American Airlines, dauke da mutum 64, ya bugi bangaren yammacin ginin tare da haddasa barna. Jim kadan bayan haka, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Amurka FAA ta rufe sararin samaniya.
Hoto: Everett Collection/IMAGO
Fasinjoji sun yi kokarin kwato jirgin
Wani jirgin United Airlines mai lamba 93 da ya nufi San Francisco, maharan suka sace tare da karkatar da shi zuwa Washington.
Bayan fasinjojin sun samu labarin sauran hare-haren ta wayoyin salula, sun yi kokarin kwato jirgin. Da karfe 10:03 na safe, jirgin ya fadi kusa da Pittsburgh dauke da mutum 44.
Hoto: David Maxwell/dpa/picture alliance
Aikin ceto a cikin hali mawuyaci
Bayan jiragen biyu sun kutsa cikin tagwayen benayen, mutanen da ke ciki suka fara kokarin tsira da rayukansu. Yayin da wuta da hayaki ke kara bazuwa, jami'an kashe gobara na birnin New York suka shiga gine-ginen domin ceto mutane. Daruruwan jami'an kashe gobara ne suka rasa rayukansu a kokarin aikin ceto.
Hoto: Jose Jimenez/Primera Hora/Getty Images/AFP
Makalewa tsakanin hayaki da wuta
Mutanen da ke saman benayen sun yi ta neman hanyar tsira, amma kuma tarkace da hayaki da wuta sun toshe hanyoyin fita. A Benen Arewa, mutane sun taru a tagogi suna kokarin samun iska. Ga da dama babu hanyar tsira, inda sama da mutum 200 suka yi tsalle daga tagogin benen domin guje wa konewa da wuta.
Hoto: Jose Jimenez/Primera Hora/Getty Images/AFP
Rushewar tagwayen manyan benayen
Da karfe 9:59 na safe, benen Kudu ya rushe sakamakon mummunar barnar da ta samu. Mintuna 29 bayan haka, Benen Arewa shi ma ya rushe, yana tayar da kura. Dubban tan na tarkace suka zubo kan titunan New York. Kusan mutum dubu uku ne suka mutu a hare-haren, ciki har da jami'an kashe gobara sama da 300 da kuma jami'an 'yan sanda da dama.
Hoto: Greg Semendinger/dpa/picture alliance
Firgici ya barke a tituna
Mutane sun rika gudu a titunan New York yayin da tagwayen benayen cibiyar kasuwanci ta duniya ke rushewa. Hazo mai tsanani na kura da tarkace sun mamaye tituna tsakanin gine-gine, sun sanya wuraren cikin duhu tare da hana mutane shakar iska yadda ya kamata. Jama'a sun yi ta kokarin tserewa daga tarkacen gine-ginen da kuma kurar da ke kara bazuwa.
Hoto: Suzanne Plunkett/AP Photo/picture alliance
Jami'an kashe gobara na aiki ba dare ba rana
Bayan rushewar tagwayen benayen, jami'an kashe gobara da na ceto sun shiga neman wadanda suka tsira a karkashin tarkacen gine-ginen. Kura da tarkace masu kauri sun mamaye yankin Lower Manhattan. Zuwa yammacin ranar 11 ga Satumba, an gano wadanda ke da alhakin hare-haren: Osama bin Laden da kungiyar Al-Qaeda.
Hoto: Dennis Van Tine/Avalon.red/IMAGO
Harin da ya haifar da gagarumin sauyi a duniya
Kwanaki shida bayan hare-haren, har yanzu hayaki na tashi daga Ground Zero, wurin da cibiyar kasuwanci ta duniya ta rushe. Tasirin harin ya wuce New York. A watan Oktoban 2001, Amurka ta fara kai hare-hare a Afghanistan da nufin kakkabe kungiyar Al-Qaeda, wanda ya zama farkon yakin Amurka mafi dadewa. A 2011, an gano shugaban Al-Qaeda, Osama bin Laden, tare da kashe shi a Abbottabad na Pakistan.
Hoto: Ringo Chiu/ZUMA/picture alliance
Hotuna 121 | 12
Wannan ya shafi ga misali, a yankin Sahel ne kungiyoyin masu jihadi suka samu damar fadada mafakarsu. Wani bincike da wata cibiya ta Critical Threats Project ta gudanar ya ambaci Nijar a matsayin misali, inda kungiyar JNIM da (ISSP) ke matsa kaimi a yankin Sahel. A kwanan baya JNIM ta kai hari a filin jirgin saman kasa da kasa na birnin Yamai, a cikin watan Yuni na wannan shekara. Al-Qaeda ita kanta ta samu rarrabuwar kawuna ta yadda wasu matasa ke fafutukar kafa daular Musulunci, a cewar kwararre mai fafutukar yaki da ta'addanci Behnam Heidenreute a kwalejin 'yan sanda ta Hamburg.
Al-Qaeda ba ta da sauran tasiri
Kwarraru dai na ganin a yanzu Al-Qaeda ba ta da karfin kai hare-hare kamar irin na 11 ga watan Satumba, sai dai rassanta misali JNIM da Al-Shabaab da AQAP na iya yin tasiri mai yawa a kasashe masu rauni. Kowa ya jaddada cewa, babu wani bayani game da al-Qaeda a halin yanzu kawai ba a san abin da take yi ba. Bugu da kari tun bayan harin da Hamas ta kai a Isra'ila a ranar bakwai ga Oktoba na 2023, abin mamaki ne yadda al-Qaeda ba ta bayyana a manyan rikice-rikicen yankin ba. Hamas da Hezbollah da Houthi da Iran, sun mamaye fagen siyasa da na soja.