1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 30 bayan hadarin nukiliya na Chernobyl

Zainab Mohammed AbubakarApril 26, 2016

An cika shekaru 30 da akuwar hatsarin cibiyar nukiliyar nan ta Chernobyl da ke kasar Ukraine wanda shi ne mafi muni da duniya ta taba gani.

Ukraine Kiew Tschernobyl Opfer Gedenken Petro Poroschenko
Hoto: picture-alliance/dpa/M.Markiv/Press Office of the President of Ukraine

Da misalin karfe 1 da minti 23 na ranar 26 da ga watan afrilun shekara ta 1986 ne dai tashar nukiliyar Chernobyl da ke kasar Ukraine ta yi bindiga. Hatsarin da ya janyo illa ga muhalli ba wai a wasu yankunan tsohuwar Tarayyar Soviet kadai ba, har da arewaci da tsakiya da kudu maso gabashin nahiyar Turai.

Mazauna Chernobly sun kauracewa matsugunansu bayan hadarin nukiliyar da ka yi shekaru 30 da suka wuceHoto: Skyba Anton Vladimirovich

Ba dadewa dai wannan ibtila'i ya bazu zuwa Belarus da Rasha da ke makwabtaka da Ukraine, bayan kwanaki biyu kuma ya isa kasashen sauran wurare ciki kuwa har da kudancin Tarayyar Jamus. Cikin 'yan kwanaki kalilan ne gajimare da ke dauke da guba ya turnuke ilahirin shiyyar arewacin duniya. Wannan dai batu ne da ba za'a taba mantawa a tarihin Turai ba.

Wannan bala'i dai a lokacin ya razana Turai, wanda a karon farko ya bude wani babi a harkar nukiliya. Kafin wannan lokaci dai ana yiwa makamashin nukiliya kallon abu muhimmi wanda ba shi da wani hadari sai dai wannan illar ta bayyana. Har ya zuwa wannan lokaci dai wasu yankunan Ukraine a gurbace suke kuma babu wanda ke zama a wurin. Har wa yau wasu nau'oi na abinci sun gurbace ba a kasar kawai ba harma da wasu yankunan tsakiya da gabashin Turai.

Tuni dai kungiyoyi na kare muhalli ke cigaba da raji na ganin an kau da idanu daga amfani da nukiliya wajen samar da makamashi duba da irin hadarin da hakan ke tattare da shi. Kasashe irin su Tarayyar Jamus sun dauki gabarar rufe cibiyoyinsu na nukuliya da ke sama musu makamashi da nufin ganin an yi maganin faruwa kwatankwacin ibtila'in da aka fuskanta a Chernobyl shekaru 30 da suka gabata.

Ana ta fafutuka wajen ganin an daina amfani da nukiliya wajen samar da makashi saboda hadarinsaHoto: dapd