Shekaru 30 bayan kisan kiyashin Srebrenica
July 11, 2025
A yau ake cika shekaru 30 na alhinin kisan kiyashin da aka yi wa Musulmi a Srebrenica na Bosnia, shekaru bayan kisan kare dangin iyalan wadanda aka kashe na ci gaba da kiraye-kirayen tabbatar da adalci. Shin su waye suka gudanar da waccan aika-aika kuma shin an hukunta su? Musa Tijjani Ahmad na dauke da waiwaye kan kisan kare dangin mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu.
A rana irin ta yau amma a 1995 da kuma ranakun da suka biyo baya aka yi wa maza da matasa sama dubu 8,000 kisan gilla a kauyen Srebrenica na Bosnia. Kotun hukunta masu aikata manyan laifuta ta duniya ta ayyana kashe-kashen a matsayin kisan kiyashi ko kuma kare dangi.
Janar Ratko Mladic na Serbia shi ne ya jagoranci kisan kiyashin, wanda kuma ke kasancewa mafi muni tun daga yakin duniya na II. Baya ga dubban mutanen da aka halaka a Srebrenica, akwai karin wasu mutanen sama da 1,000 da suka yi batan dabo.
Kodayake Kotun Duniya ta yanke hukunci kan wasu daga cikin wadanda suka gudanar da waccan aika-aika ciki har da Janar Mladic, har yanzu ya zuwa wannan lokaci wasu mutanen na bukatar adalci.
Akwai kaburbura sama da dubu 7,000 a makabarta ta Srebrenica-Potocari Memorial da ke gabashin Bosnia. Yaki ya barke a Bosnia and Herzegovina tun bayan ballewar Yugoslavia wanda kuma ya ruruta rikici tsakanin kiristocin Orthodox na Serbiyawan Bosnia da kuma musulmin Bosnia tun daga 1992 zuwa 1995.
Duk da cewa a 1993, MDD ta girke dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin na Srebrenica inda ta ce yankin ba ya fuskantar barazanar tsaro, amma daga bisani sojojin Serbia sun sake kutsawa yankin domin ci gaba da kisan gilla kan dubban tsirarrun kabilu.
MDD ta kasa kare musulmin Bosnia. To amma daga bisani kasar Netherlands ta bai wa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su sama da 8,000 hakuri kan gazawar dakarun kasarta da ke aikin wanzar da zaman lafiya.
Shekaru bayan kisan gillar, a shekarar 2001 da 2007, Kotun Duniya ta ayyana yakin Srebrenica a matsayin kisan kare dangi.
A watan Nuwambar 2017, iyaye da matan wadanda aka kashe sun kalli yadda kotun ICJ ta yanke hukunci kai tsaye ta kafar talabijin ga mutane 45 da suka aikata kisan kiyashin ciki kuwa har da Janar Ratko Mladic, wanda yake fuskantar daurin rai da rai a gidan wakafi.
Kasar Serbia ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ki amincewa da abin da ya faru a ranar 11 ga watan Yuli a matsayin kisan kare dangi.