Yara na fuskantar azabtarwa a wasu sassan duniya
November 20, 2019Nyabenda Emmanuelle da maigidanta Misago Jean Marie sun kasance cikin rudani a Bujumbura babban birnin Burundi lokacin da abokan karatun 'yarsu, suka iske su da mummunan labari cewar Shadia ta suma a makaranta. Sai dai yarinyar 'yar shekara 13 ta mutu a lokacin da ake kai ta asibiti. Iyayen sun ce akwai raunuka da yawa a jikin Shadia, ko da shi ke shugaban makarantar ya ce farfadiya ce ta yi ta mutu. Amma a cewar Shugwejimana Beliene 'yar uwar yarinyar ta ce tana da shaidu da ke nuna cewar malami ne ya azarbtar da ita.
Azabtar da yara a cikin makarantu a wasu sassan nahiyar Afirka ya yi kamari
“Daya daga cikin abokan karatun ta ta fada min cewa Shadia ta sha dan karen duka daga malaminta, lokacin da ta kasa gane amsa bayan da aka tura ta gaban babban allon rubutu. Shadia ta ce ba ta da masaniya, sannan malamin ya doke ta da sanda a wuya, da kuma a baya. A lokacin da ta dawo kan kujerarta, ta fadi a kasa, ta suma kuma jini na zuba a jikinta. "Ba a cika samu mace-macen yara sakamakon azabtar da su ba, amma hukunta yara idan suka yi laifi na ci gaba da zama ruwan dare a kasashe da dama na Afirka. A Burkina Faso ma dai, babu wata doka da ta haramta zane yaro a matsayin hanyar ilimantarwa a makarantu. Ko da Palenfo Goro jami'a a ofishin walwalar jama'a a Burkina Faso ta ce doka na ba da damar bugon yaro ba tare da ji masa ciwo ba, ko a makaranta ne ko a gida. Sai dai Sonia Vohito ta hukumar da ya ke yaki da azabtarwa a duniya ta ce akwai bukatar doka ta hana amfani da azabtarwa a harkar ilimi, inda ta ce ya kyautu dokar ta tanadi hukunci mai tsanani.
"Yarjejeniyar ba ta fito fili karara dangane da azabtarwa ba. Kasancewa a cikin 2006 kwamitin ya ce hakan zai taimaka sosai a Afirka. Amma idan aka ce hujjar da ake bayarwa wajen hukunta yara iri daya ce a Afirka da Turai. Za ka yi mamaki."
Wasu kasashen Afirka na yin dari-dari wajen amincewa da dokar azabtar da yara
Sai dai kasashen Afirka na jan kafa wajen amincewa da dokokin da ke haramta dukan yara a makarantu da gida. Ko da a Najeriya inda aka bankado makarantun da ke amfani da azabtarwa wajen gyara halin kangararru ba a kai ga fara aiwatar da dokar ba duk da cewar akwaita. Tsofuwar ministar ilimin Najeriya Obiageli Ezekwesili ta bayyana cewar jihohin arewacin kasar ne suka kasa fara amfani da wannan doka duk da cewar a yankinsu wannan matsalar ta fi kamari. "Muna da doka da ke kare hakkin yara da aka kafa, wadda ke bukatar aiki da ita a cikin jihohi dabam-dabam na kasar. Akasarin jihohin da ke kudancin suna aiki da ita, a wasu wuraren ma, sun kafa
tasu dokar baya ga ta gwamnatin tarayya. Amma dai yawan jihohi na arewaci ba su yi hakan ba. "
A watan Satumban da ya gabata, an ceto fiye da kangarurru 300 daga makarantun gyara hali a cikin Jihar Kaduna, da kuma a cikin watan Oktoba a Jihar Katsina, lamarin da ya sa Najeriya kaurin suna a fannin rashin mutunta hakkin yara. Shekaru talatin bayan yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya game da Hakkin yara, kasashe takwas na Afirka ne kawai suka dakatar da azabtar da yara, inda Afirka ta Kudu ta kasance karshe ta baya-bayan nan da ta shiga sahu a watan Satumba. Sai dai Burundi da Burkina Faso suna ci gaba da ba da izinin hukunta yara a gida ta hanyar. Yayin da Togo ta kasance ta farko a Afirka a 2007 da ta hana dukan yara kwata-kwata a gida ko a makaranta.