Bikin cika shekaru 30 da hadewar Jamus
November 9, 2019![Deutschland Gedenkfeier zum Mauerfall in Berlin - Steinmeier dankt Osteuropäern](https://static.dw.com/image/51179090_800.webp)
Daga cikin shugabannin kasashen da suka halarci bikin akwai Sulobakiya Poland Jamhuriyar Chek da Hungary na daga cikin manyan baki da suka kasance tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin a yayin bukin.
Baya ga wasu kasaitattun bukukuwan a yau din nan shi ma shugaban kasar Frank-Walter Steinmeier ya gabatar da wani jawabi a gaban dandazon jama'a a kofar Brandebourg, a yayin da ita kuwa shugabar gwamnati Angela Merkel ta gabatar da jawabinta a Bernauerstrasse, wurin da ke zaman matsirin soma ginin katangar ta Berlin da ta raba bangarorin biyu a ranar 13 ga watan Agustan 1961.
Sai dai masu sharhi na ganin wasu shugabannin manyan kasashen duniya abukan dasawar Jamus basa cikin wadanda suka halarci bukukuwan na wannan rana, a yayin da aka bayyana shugaban Faransa Emmanuel Macron da cewar zai halarci wata ganawa ne kawai a ranar Lahadi domin cin abincin dare da hukumomin na kasar Jamus, inda a share daya tuni sakataren harkokin wajen Amirka ya kammala ziyarar sa a yammacin jiya.