1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Sake zama kasa daya

Fürstenau Marcel PUG, AS, LMJ
November 8, 2019

A ranar tara ga watan Nuwamba na shekara ta 1989 aka kawo karshen yakin cacar baka tsakanin maasu mulkin danniya da kuma masu rajin kare dimukuradiyya.

Wende DDR - Mauerfall - Kanzler Kohl in Berlin am 10.11.1989
An sha tsallen murna bayan rushewar bangon BerlinHoto: picture alliance/dpa/M. Kainulainen

Rabuwar Jamus ta Gabas da ta Yamma a shekarun baya wata alama ce ta rashin jituwa tsakanin masu bin ra'ayin kwamunisanci da wadanda ake kallo a matsayin 'yan jari hujja. To sai dai shekaru 30 da suka gabata wannan lamari ya sauya inda kasar ta hade waje guda. Hadewar da bangarorin byiu suka yi dai ta tabbata ne bayan da kasashen Yamma da suka hadar da Amirka da Birtaniya da Faransa da ke mara baya ga Jamus ta Yamma da kuma Tarayyar Soviet wadda Jamus ta Gabas ke karkashinta suka amince da hakan.

Gorbachev  ya kawo sauyi

Wani abu har wa yau da ya taimaka wajen kai wa ga wannan mataki shi ne irin sassaucin da aka samu a yankin Soviet musamman ma bayan da Michail Gorbachev ya sakarwa kasashen da ke bin tsarin Kwamunisanci mara sabanin yadda abin yake a baya, inda ya ce ya tabbata kowacce kasa za ta iya yin abin da ya dace da ita.

Michail Gorbachev tsohon shugaban tsohuwar Tarayyar SobietHoto: Getty Images/AFP/O. Andersen

Wadannan kalamai na Gorbachev ne dai ya sanya mutane da dama ciki har da Axel Klausmeier masanin tarihi a Jamus kana shugaban gidan adana kayan tarihi na rabuwar Jamus a Berlin, ganin hawansa kan gadon mulki ya haifar da sauyi babba wanda kasashe da dama suka sauya irin tafiyar da suke yi.

 

Zanga-zanga ta cimma nasara

 

Wannan yanayi da aka shiga dai ya sanya kasashe da dama a yankin Soviet nuna alamun fara neman sauyi na irin tsarin da ake bi wajen gudanar da sha'anin mulki da ma sha'anin zirga-zirga tsakanin kasashen yankin gabashi da yammaci da kuma rage irin yadda jami'an leken asiri ke sanya idanu kan al'umma musamman ma kasashen gabashin Turai. Hakan ne kuma ya bude kafa ta fara gudanar da zanga-zanga ta neman sauyi a Jamus ta Gabas, inda jama'a suka rika fita don yin zanga-zanga ta neman rushe katangar da ta rabasu da sauran kasashe musamman ma Jamus ta Yamma.

Rushewar katangar Berlin ya janyo sake hadewar Jamus ta Gabas da ta YammaHoto: picture-alliance/akg-images /Schuetze /Rodemann

 

Da yake tsokaci akan wannan batu, masanin tarihi Axel Klausmeier ya ce irin yadda al'umma suka rika fafutuka ba ji ba gani ne ya sanya mahukunta mika kai bori ya hau, musamman ma dai da ya ke yawan masu zanga-zangar ya wuce misali.


"Fargabar da ake da ita ta karu a ranar tara ga watan Oktoba musamman ma a birnin Leipzig, domin ba a san yadda mahukunta za su yi da mutanen da ke zanga-zanga wadanda yawansu ya kai dubu 70 ba. Sakamakon rashin yin wani abu ga mutanen dai ya sanyasu jin cewar hakarsu za ta kai ga cimma ruwa."

 

Wannan hali da aka shiga dai shi ya taimaka aka kawo karshen rabuwar Jamus ta Gabas da ta Yamma shekaru 30 din da suka gabata, lamarin da ya haifar da murna maras adadi tsakanin al'ummar kasar. To sai dai duk da cewar an hade, ya zuwa yanzu da dama na ganin akwai 'yan banbamce-banbamcen da ke akwai tsakanin yankin gabashin kasar da na yammaci, musamman ma dai ta fuskar tattalin arziki.