1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaKamaru

Kamaru: Shekaru 40 da ibtila'in Tafkin Nyos

August 21, 2026

Shekaru 40 da samun sinadarai masu guba daga cikin Tafkin Nyos na kasar Kamaru, inda kimanin mutane 2,000 suka halaka lokacin da suke barci.

Kamaru | 1986 | Bala'i | Iska mai Guba | Tafkin Nyos | Shekaru 40
Yadda Tafkin Nyos ya kasance a ranar 27 ga watan Agustan 1986Hoto: Clément Tjomb/AFP

Shekaru 40 da suka gabata a daren ranar 21 ga watan Agustan shekara ta 1986, Tafkin Nyos ya fitar da sinadari da ke dauke da guba mai yawan gaske. Sindaran sun watsu cikin kauyukan da ke yankin, tare da halaka mutane da dabbobin da ke barci. Yankin da keArewa maso Yammacin Kamaru, na da nisan kilomita 315 daga birnin Yaoundé fadar gwamnatin kasar.

Bala'i kwance a karkashin kogi

An hakikance Tafkin Nyos ya yi aman wuta, shekaru aru-aru da suka gabata. Akwai fiye da mutane 3,000 da suke rayuwa da iyalansu a kewayen tafkin, inda suke noma da kiwo. Bala'in ya halaka kimanin mutane 1,700 da dabbobi fiye da 3,500, abin da ke zama bala'i mafi girma da Kamarun ta fuskanta a tsawon tarihi. Masanin kimiyyan ma'adanai da ke jami'ar Yaoundé Farfesa Isaac Konfor Njilah ya ce, bala'in ya faru ba-zato ba-tsamman.

Wasu yara da suka tsira daga ibtila'in gurbatacciyar iska a Tafkin NyosHoto: Mike Nelson/AFP

Bayan faruwan lamarin, masana kimiyya daga Kamaru da sauran kasashen duniya sun kaddamar da gagarumin binciken gano musabbabin faruwan wannan bala'i. Sun gano cewa, gurbatacciyar iskar ta dade tana kwance a nisan fiye da mita-200 kasan kogin tsawon kwashe shekaru. Tsang Emelda Njah tana cikin wadanda suka tsira daga wannan bala'in kuma ta ce, har yanzu tana tuna lamarin shekara 40 bayan afkuwarsa.

Gaza daukar matakin riga-kafi?

Shekaru biyu gabanin bala'in na Nyos na shekara ta 1986, an ga alamomi. A ranar 15 ga watan Agustan shekara ta 1984 ana fuskanci makamanciyar iskar da ta gurbata a yankin Arewa maso Gabashin Nyos, abin da ya halaka mutane 37. Daga bisani bayan bala'in, masana sun yi aikin kwashe gubar sannu a hankali.

Fassara: Suleiman Babayo

Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar