Iran bayan shekaru 40 na juyin juya hali
February 11, 2019Talla
Miliyoyin al'umma ne ake sa rai za su fita gangami a wannan rana ta Litinin a kasar Iran a yayin bikin tunawa da shekaru 40 na juyin-juya halin Islama da ya yi awon gaba da gwamnatin Shah Mohammed Reza Pahlavi da girka jagoranci na Shugaban addini Ayatollah Khomeini a shekarar 1979.
An dai tsaurara matakan tsaro a dukkanin fadin kasar gabanin gangamin bikin na Litinin. A shekara bara dai aka kai wani hari a lokacin da sojoji ke gudanar da wani maci. Harin da ya yi sanadi na rayukan mautane da dama.
Kafin dai wannan rana shugaban na addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi zafafan kalamai ga Amirka sai dai ya sake jadadada cewa kalaman nasa raddi ne ga shugabanni a Amirka ba al'ummar kasar ta Amirka ba.