1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 50 na Sarkin Kano kan gadon mulki

Usman ShehuJune 14, 2013

Alhaji Ado Bayero dai shi ne sarki na sha uku a jerin sarakunan Fulani na jihar Kano. A ranar goma ga watan Oktoban shekarar ta 1963 aka nada shi a matsayin sarkin na Kano.

Hoto: Thomas Mösch

A bana ne dai Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya cika shekaru hamsin ya na rike da matsayin sarkin Kano kuma shi ne sarki na goma sha uku a jerin sarakunan Fulani a Kano din.

Alhaji Ado bayaro dai wanda a baya wakilin doka ne kafin daga bisani ya kasance jakadan Najeriya a kasar Senegal, ya hau kan karagar mulkin ta Kano ne lokacin da ya ke da shekaru talatin da uku da haihuwa.

An nada mai martaba sarkin ne a kan wannan matsayin a ranar goma ga watan Oktoban shekarar ta 1963. Sakamakon kwashe tsawon wannan lokaci a kan karagar mulki ne dai ya sanya aka shirya gudanar da bukukuwa domin taya sarkin murna.

Fadar sarkin KanoHoto: Tanja Suttor-Ba

Daga cikin jerin abubuwan dai akwai addu'o'i wanda aka gudanar a babban masallacin Juma'a na Kano domin yin godiya ga Allah madaukakin sarki da Ya sanya Alhaji Ado Bayero ya kwashe wannan lakaci kan gadon mulki tare ma dai da addu'ar neman karin lafiya ga gare shi.

Baya ga wannan an shiya hawan daba a wannan Asabar din duka dai da nufin karrama sarkin wanda ke da matukar kima a idanun al'ummar jihar Kano da ma dai Najeriya baki daya. An gayyaci mutane da dama daga ciki da wajen Najeriya domin hallartar hawan na daba.

Ziyarar Shugaba Jonathan a fadar Sarkin KanoHoto: picture-alliance/dpa

Rashin hulda da abokan yaranta ita ce damuwar sarkin Kano

Yayin da ya yi wata ganawa da manema labarai gabannin fara wadannan bukukuwa, Sarkin na Kano ya nuna matukar godiyarsa ga Ubangiji da ya sanya shi ya yi tsawon rai har ya kai ga ganin shekararsa ta hamsin a gadon sarauta.

A cikin ita dai wannan ganawa, Alhaji Ado Bayero ya ce a tsawon wannan lokaci da ya shafe ya na kan gadon muliki babu wani abu guda dai zai iya cewa ya zame masa wani abu da zai yi nadamarsa sai dai ya ce abu guda da ya dan sosa masa rai iya shekarun nan a mastyainsa na sarki shi ne rashin samun sukunin yin hulda ta kut da kut da abokansa wanda su ka taso tare su ka kuma yi wasan kasa lokacin da su ke yara.

Guda daga cikin dadaddun gine-gine sarauta a KanoHoto: DW

Tarihi dai ba zai mance da Alhaji Ado Bayero ba a mastyin sarkin da ya fi dadewa ya na jagorantar al'ummar Kano. Sarkin dai a halin yanzu ya na da shekaru tamanin da uku da haihuwa, ya na kuma da mata da 'ya'ya gami da jikoki da dama.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe