Shekaru 60 bayan juyin mulki na farko a Najeriya
January 15, 2026
A rana 15 ga watan Janairu 1966 aka kashe Firimiyan jihar Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna yana da shekaru 55 a duniya, tare da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa, a yunkurin sojoji na wancan lokaci ga juyin mulki.
Tun a wancan lokaci 'yan Najeriya na tunawa da irin gudunmawa da muhimman abubuwan ci gaba da Gamji mazan fama ya kawo ga ci gaban yankin Arewa.
Dr. Ibrahim Usman Isa masanin zamantakewa da tarihi ne ya yi bayani akan wasu abubuwa da ake tuna Sardaunan da su.
A jihar Sokoto dai, duk shekara albarkacin tunawa da Ahmadu Bello Sardauna a hukumance ana shirya tarukan lakcoci ga dalibban makarantun Boko da na Addini. Ahmad Baba Altine shi ne shugaban hukumar Ilimin larabaci da suke shirya wannan lakca.
Shi ma dai masanin kimiyyar siyasa a Jamia'ar Usmanu Danfodio Sokoto Farfesa Yahaya Tanko Baba ya ce Saradunan na da wuya a iya cike gibin da ya bari.
A jihar Sokoto dai kamar sauran yankin arewa, mutane na cewa tarihin Sardauna kusan abu ne da ake bitarsa cikin zukata, saboda yadda al'umma ta ribantu da rayuwarsa
Yayin da Ahmadu Bello Sardauna ke cika shekaru 60 da kwanta da dama, mutane na tururuwa zuwa gidan tarihi na Waziri Junaidu da ke Sokoto domin kallon motar da ya yi amfani da ita