1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyin mulkin farko a Afirka

January 13, 2023

A ranar 13 ga watan Janairu 1963 ne sojoji suka kifar da gwamnatin farko a Togo, tare da kisan shugaban kasar na wacan lokaci Sylvanus Olympio.

Togo Politiker Sylvanus Olympio
Hoto: United Archives/imago images

Babu wani kasaitaccen biki da hukumomi a birnin Lome suka shirya domin tunawa da jagoran dimukuradiyar Sylvanus Olympio, wanda wasu sojojin suka yi wa kisan gilla a ranar 13 ga watan Janairun 1963, shekaru biyu kacal bayan zabensa a matsayin shugaban kasa.

Shugaba Olympio ya kwanta dama a hannun wata bataliyar soji ne a yayin da yake kokarin samun mafaka a ofishin jakadancin Amirka de birnin Lome, lamarin da ya haifar da tarin tambayoyi ga mabiya harkokin siyasa.

Sai dai ga Horatio Freitas tsohon ministan Togo da ke matashi a yayin kisan gillar, mutuwar tsohon shugaban ba ta rasa nasaba da makarkashiyar siyasar uwar gijiyar Togon wato Faransa.

 

"Shugaba Olympio ya kai ziyarar farko a kasar Jamus inda ya gana da shugaban gwamnati Konrad Adenauer. daga nan ya wuce zuwa Amirka don tattaunawa da takwaransa John F Kennedy. bayan kai wadaddan ziyarce-ziyarcen ne, ya kai ziyara a Faransa, Shugaba Charles de Gaulle bai ji dadin irin yadda kasar da Faransa ta yi wa mulkin mallaka kwanaki bayan 'yancin kai ta shiga neman kulla hulda da wadannan manyan kasashen ba. Daga nan ne fa duk wasu masu karfin fada a ji a Faransa, suka shiga kulla wa gwamnatin Olompio makrkashiya don kifar da ita, wanda hakan ya kasance juyin mulki na farko a kasashen Afirka renon Faransa a shekarar 1963."

 

Bayan mutuwarsa jam'iyar UFC wato Union des forces du changement da ta kasance gamin gambizar jam'iyyun siyasar farko a Togo, ta ci gaba da aiki.

Ta kasance babbar jam'iyyar adawa da ta kafa tarihi a Togo, dan marigayi Olompio Gilchrist Olympio na hankorin bin tafarkin mahifinsa ta akidar siyasa.

Ko da ya ke ga Elliot Ohin tsohon minista kuma kusa a jam'iyyar UFC, ba Gilchrist Olympio kadai ba ke rike da tafarkin mahifinsa, su ma dai sun dukufa kan wannan tafarkin na tsohon shugaban da aka yiwa kisan gilla.

 

"A matsayinmu na 'yan baya, muna dorawa daga inda aka tsaya, muna tsammanin dawo da abinda ya gabata, kuma ma dai kamata ya yi mu amfana da abubuwan da suka gabata don kaucewa kura-kuran 'yan baya  da zummar gina sabuwar rayuwa, ina ganin manufofi da akidodin Sylvanus Olympio na da matsaya har a wannan lokaci."

Shugaba Sylvanus Olompio dai ya kasance maicike da burin zartar da manufofin siyasa irin na inganta rayuwar al'umma, wanda har yanzu ake alfahari da ita. In ji  Ekoué Folly Gada malami a jami'ar birnin Lome.

 

"Shekaru 60 da suka gabata har yanzu ba cimma wasu burrukan da shugaba Sylvanus Olympio ya sakawa gaba ba, manufofinsa na nan har yanzu a zahiri, kana suna kasancewa babban kalubale a wadannans shekaru."

Shekaru fiyde da 60 bayan kisan gillar, har yanzu ana kasa gudanar da takamaimen bincike da ma zartar da hukunci kan sojojin da suka kifar da gwamnatin ta farko a tsarin dimukdariyyar Togo, duk da yake ga jam'iyyarsa ta UFC marigayi Gnassingbé Eyadema da kitsa juyin mulkin.

 Jam'iyyun siyasa na dawa da sauransu sun sun shirya tarukan tunawa da gwarzon dimukuradiyar Togon, baya ga shirya masa addu'i'i a daidaikun wuraren ibada.