1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shekaru 61 da samun 'yancin kai a Nijar

August 3, 2021

A ranar Talata uku da watan Agusta, Jamhuriyar Nijar ke cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Faransa. Wasu 'yan kasa dai na yabo wasu kuma na suka.

Deutschland l Besuch des Nigerianischen Präsidenten in Berlin
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Bisa al’ada a jajibirin ranar shugaban kasar ke gabatar da jawabi  ga ‘yan kasa da ake kira “message à la Nation”, jawabin da ke tabo batutuwa masu mahimmanci game da rayuwar ci gaban kasa.

A daren Talatar ma dai shugaban kasar Bazoum Mohamed, ya yi jawabin da ya dauki hankulan ‘yan kasar, inda a bana Damagaram ke karbar bakuncin bikin a matakin kasa.

Jim kadan da kammala jawabin masana tsirrai ta bakin Kanar Sani Ado mai ritaya ya ce maye shuka itatuwan zogale abun dubawa ne.

Kamar ko wace shekara dai a irin wanan rana ta zagayowar tuni da samun ‘yan cin kai ‘yan kasar ke bayyana ra’ayoyi a kan batutuwan da suka shafi kasarsu ta gado.

Wasu daga cikin su sun yaba da tafiyar gwamnati kasar wacce ba ta jima da kama mulki ba, yayin kuma da wasu ke cewa lallai ne a sake lale na daga tafiyar siyasar kasar da kullum ke jiya i yau.