Najeriya ta cika shekaru 61 da 'yanci
October 1, 2021
Talla
A shekarar 1960 Najeriya ta samu 'yancin kai bayan mamayar da Turawan Birtaniya suka yi mata tun a shekarar 1901, wato shekaru 59 na mulkin mallaka.
Dr. Nnamdi Azikiwe shi ne shugaban kasa na farko a mulkin farar hula, Sir Abubakar Tafawa Balewa ya zama firaminista, sai dai an kifar da gwamnatinsu shekaru uku bayan fara aiki. A shekarar 1999 gwamnatin farar hula ta sake dawowa a shekarar 1999, bayan shafe shekaru na mulkin soja.