1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceJamus

Jamusawa bakaken fata sun azabtu a gun Nazi

May 8, 2025

A daidai lokacin da ake cika shekaru 80 da kawo karshen mulkin Nazi a Jamus, wani sabon rahoton DW ya yi waiwaye kan yadda bakaken fata da ke da tsatso da Afirka da ake kira Afro-German suka sha ukuba wancan lokaci.

Jamus | Nazi | Azabtarwa | Jamusawa | Bakaken Fata | Shekaru 80
Bikin cika shekaru 80 da kawo karshen mulkin 'yan Nazi a JamusHoto: ODD ANDERSEN/AFP/Getty Images

A lokacin mulkin 'yan Nazi a Jamus, bakaken fata da ake kira Afro-German sun fuskanci wariya da daukar matakan hana su haihuwa da kuma hana su shaidar zama 'yan kasa. Masu fafutukar kare hakkin dan Adam da masana, na fafutukar ganin an yadda da rashin adalcin da 'yan Nazin suka yi wa Jamusawa bakaken fatar. A cewarsu, har ya zuwa wannan lokaci bakaken fata na fuskantar tasirin wariyar launin fatar. Jamus ta fara alaka da Afirka kai tsaye tun daga 1880 kimanin shekaru 145 da Turawan mulkin mallakar kasar suka baza komar cinikin bayi a kasashe kamar Kamaru da Togo da kuma kasashen Gabashin Afirka da ke karkashin ikon Jamus har ma da Namibiya da ta kubucewa Jamus a lokacin yakin duniya na daya.

Karin Bayani: Daga mulkin mallaka zuwa wariyar launin fata

Duk da cewa babu kididdiga, amma dubun-dubatar bakaken fata ne aka yi jigilarsu daga Afirka da yankin Caribbean da kudancin Amurka zuwa Jamus. Masana tarihi sun rubuta tarin littattafai kan ta'asar da Jamus ta yi na nuna kyama ga bakaken fata da Yahudawa da Romawa har ma da sauran tsirarru a kasar, kama daga batun wariyar launin fata da kisan kiyashi har ma da keta hakkin masu neman jinsi da sauran tsirarru. Tun daga shekara ta 1880 kawo yanzu, Jamus ta gaza kawar da tasirin kyamar da ake nuna musu. Farfesa Katharina Oguntoye da ke nazari kan tarihin Jamus a Berlin babban birnin kasar ta ce, akwai banbamci tsakanin tasirin mulkin mallaka kan shekarun da aka kwashe ana aikata ta'asar da kuma wariyar launin fata.

To amma ga Robbie Aitken masanin tarihi a Jami'ar Sheffield Helen da ya shafe shekaru sama da 20 yana nazari kan tarihin Jamus ya ce, wariyar launin fata ta samo asali ne tun daga lokacin mulkin mallaka a 1929 har zuwa kafa gwamnatin Nazi a 1933. Bakaken fata na da tarihin fuskantar cin zarafi da tsangwama, daga fararen fata. Farfesa Aitken ya ce tabbas akwai yunkurin kawar da bakaken fata daga doron kasa daga gwamnatin Adolf Hitler ta la'akari da kisan kiyashin da jami'an 'yan sandan farin kaya na Nazi da aka fi sani da Gestapo, suka yi wa mutane da dama ciki har da kananan yara. Ga misali wani dan asalin Kamaru Mandenga Diek da ya yi fice a harkar kasuwanci a kasar Jamus kafin zuwan gwamnatin Nazi, ya rasa dukkan dukiyar da ya mallaka ta kuma haramta masa kasancewa dan kasa da shi da iyalansa daga gwamnatin Nazi.

Karin Bayani: Jamus: Tuna 'yantar da sansanin Nazi a Buchenwald

A kokarin hukumomi wajen ganin sun killace tarihin mulkin mallakar Jamus a Afirka, a shekara ta 2022 an bude gidan tarihin bakar fata a birnin Cologne mai suna Theodor Wonja Michael da ya yi gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata tun daga wajen karni na 20. To amma ina mafita kasancewar kaddara ta riga fata? Farfesa Oguntoye ta jami'ar Berlin ta bukaci karfafa koyar da tarihin bakaken fata tare da sanya shi a manhajar makarantu. Baya ga wannan shawara ta karfafa karatun tarihi a makarantu akwai kuma bukatar samar da mutum-mutumi, domin tunawa da bakaken fatan da suka yi shura a lokacin mulkin mallaka a birnin Berlin.