Shekaru 80 da 'yantar da sansanin Auschwitz
January 27, 2025
A wannan rana ta 27 ga watan Janairu aka cika shekaru 80 da 'yantar da sansanin gwale-gwale na Auschwitz da sojojin Nazi na Jamus suka yi amfani da shi wajen kisan kimanin mutanen milyan daya da dubu-dari daya a lokacin yakin duniya na biyu.
Karin Bayani:Duniya na bikin cika shekaru 80 da 'yantar da sansanin gwali-gwali na Auschwitz
A Poland mai mutane kimanin 10,000 da Jamus ta kame a shekarar 1939 ta sake masa suna zuwa Auschwitz. A wajen sojojin Jamus na Nazi sun kafa sansanin kisa mafi girma na Auschwitz-Birkenau tun daga shekarar 1941. Sahihan bayanai da aka samu sun tabbatar da cewa 'yan Nazi sun halaka kimanin mutane milyan da dubu-dari daya zuwa karshen watan Janairun shekarar 1945 kuma galibi Yahudawa amma akwai 'yan Roma da Sinti gami da wasu tsirarun al'uma. Me aka yi a wajen? Me ya saka Auschwitz? An zabi wajen saboda ya kasance a tsakiyar Turai inda za a iya kai mutane ta jiragen kasa, wannan na daga cikin abubuwan da aka duba.
Christoph Heubner mataimakin shugaban kwamtain Auschwitz na kasa da kasa ya yi karin haske:
Karin Bayani:Shekaru 75 da kawo karshen sansanin Nazi a Auschwitz
"Kalmar Auschwitz tana tafiya kut-da-kut da korar mutane, an zabi wurin saboda yana tsakiyar Turai, zai zama inda za a yi safarar mutane daga kowane bangare ta hanyar jiragen kasa, domin haka an duba hanyar zuwa."
Jim kadan bayan farmaki dakarun Jamus karkashin shugaban gwamnati Adolf Hitler sun kwashe yankunan kasar Poland, inda aka kashe mutane da dama lokacin harbe-harbe a gabashin Poland. Akwai lokacin da aka kashe Yahudawa 900 kusa da birnin Riga. Kuma lokacin aka tsara wannan sansani, tun daga shekarar 1942 an kara yawan jiragen kasa da suke kwasar Yahudawa daga bisani sai mutanen su bace, wadanda ake kashewa a yankunan Poland da aka mamaye.
Christoph Heubner mataimakin shugaban kwamtin Auschwitz na kasa da kasa ya ce wannan gagarumin kisa ne da gwamnati ta kitsa:
Karin Bayani:Musulmai a sansanin gwale-gwale
"Wuri da gwamnati ta tsara aikata laifuka, kuma aka aikata laifin ta hanyar kashe mutane masu yawa, kuma wasu mutanen da aka ware, wato Yahudawa, 'yan Sinti da kuma Roma gami da wasu."
Daga bisani an gano cewa galibin jiragen kasa da suke kwaso mutane suna karewa a sansanin Auschwitz wadanda suka fito daga Jamus da wasu sassan Turai. Jiragen da ake cewa suna dauke da fursunoni sun kasance mutanen da ake kai su inda ake kashe su. Sojojin Tarayyar Soviet a ranar 27 ga watan Janairun 1945 da suka kwace sansani kafin kawo karshen yakin duniya na biyu sun jijjiga da abin da suka gani kamar yadda Christoph Heubner ke cewa:
Karin Bayani:Musulmi da Yahudawa sun ziyarci Auschwitz
"Wannan lokaci ne da komai ya tsaya. Su kansu wadanda suka yi ceton a kofar shiga Auschwitz, matasan sojoji Tarayyar Soviet daga Ukraine da kuma Rasha da sauran jamhuriyoyin Tarayyar Soviet a lokacin, ba su yarda da abin da suka gani da idonsu ya gani ba. Sun ga abubuwa da yawa da suka hada da gawawwakin mutanen da suke tsaye kan kafafunsu, gami da kwarangwal na mutanen da suke raye. Wannan tsayuwa cik na 'yan wasu dakikai, na wadanda suka kawo ceto inda wasu suke ciki kan wasu suke tsaye a bayan shingen sansanin."
A biranen Jamus da dama irin Kolon, da Stuttgart, da Hamburg, da Wiesbaden gami da Berlin an kafa wuraren tunawa da mutanen da aka kwasa zuwa sansanin da aka halaka su lokacin yakin duniya na biyu.