1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
TarihiJamus

Majdanek: Sansanin gwale-gwale mafi muni

Pieper Oliver MAB/LMJ
July 24, 2024

Shekaru 80 ke nan, bayan kubutar da sansanin gwale-gwale da ke kusa da Lublin da sojojin Tsohuwar Tarayyar Soviet suka yi. Wani dan jarida daga Amurka, ya kwatanta yanayin da fagen yaki mafi muni a duniya.

Shekaru 80 | 'Yantarwa | Sansani | Gwale-Gwale | Majdanek
Sansanin gwale-gwale na Majdanek da aka 'yantar shekaru 80 da suka gabataHoto: Staatliche Museum Majdanek

Daga bisani bayan kubutar da sansanin gwale-gwalen na kusa da Lublin, an gina sansanin tunawa da wadanda suka riga mu gidan gaskiya a yakin duniya na biyu a Majdanek. Masu matsakaicin ra'ayin gurguzu sun yi kokarin boye kisan gillar da aka yi wa mutane dubu 78, ciki har da Yahudawa kusan dubu 60 da kuma 'yan Polanda da 'yan Belarus da 'yan Ukraine da aka tsare tare da kona gine-ginen da suke ciki. Ko da Wieslaw Wysok da ke zama mataimakin daraktan gidan tarihi na Majdanek sai da ya bayyana cewa an gano wasu shaidu masu ban tsoro game da laifukan da Jamusawa suka aikata, kama daga kasusuwa da gawarwakin mutane da kuma fursunonin da aka kashe wadanda galibinsu Yahudawa da kuma 'yan Poland ne.

Karin Bayani: Bikin tunawa da nasara a kan sojojin NAZI

Akwai dakuna dauke da alamun da ke nuna irin ta'asar da aka aikata da suka fito fili, kama daga dakin da ake fesa gubar gas da wuraren da ake kona gawarwaki da kurkuku da dubban takalma. A karshen watan Yulin 1944 watanni shida kafin 'yantar da sansanin gwale gwale na Auschwitz, ya tabbata cewar kisan Yahudawa da 'yan Poland ba farfagandar ta yaki ba ce abu ne na zahiri. An gina sansanin Majdanek ne bisa umarnin wani jagoran 'yan Nazi Heinrich Himmler a shekarar 1941, a matsayin wuri mai muhimmanci na salwantar da rayuka. Stephan Lehnstaedt malamai a fannin nazarin kisan kare dangi da aka yi wa Yahudawa a jami'ar Touro ta Berlin, ya nunar da cewa shelkwatar Aktion Reinhardt ta Lublin da ake hada-hadar tattalin arziki a nan ne ake rarraba Yahudawan da ake bukata domin gudanar da aikin karfi da ake son su yi. A nan ne ake jera kayayyakin da aka sace, sannan a kara sarrafa su.

Daga nan ake jigilar mutane zuwa wasu sansanonin kuma daga can ne ake tsara komai. Sansanonin na gwale-gwale ba su da alaka da barikin soja amma abin da ya faru a Majdanek ba sirri ba ne a Lublin, saboda 'yan gudun hijira da ma'aikata farar hula sun ba da rahoto game da abubuwan da suka faru. A watan Agustan 1944, an bai wa 'yan jarida na farko na yammacin Turai damar ziyartar sansanin, inda mujallar Amurka mai suna "Life" ta buga wani rahoto kan Majdanek mai taken "Mafi munin misali na tsarin zalunci a tarihin wannan zamani." Amma Stephan Lehnstaedt malamai a fannin nazarin kisan kare dangi da aka yi wan Yahudawa a jami'ar Touro ta Berlin ya ce, wannan bai yi tasiri a yakin duniya ba.

Karin Bayani: Ziyarar manyan wakilan Musulmai da Yahudawa a sansanin Auschwitz

Majdanek ba wai ya kasance sansanin halakarwa na farko da sojojin tarayyar Soviet suka mamaye ba, amma yazama wurin tunawa da sansanin farko a duniya na tunawa da wadanda rikici ya rutsa da su. Sai dai sannu a hankali, ana ci gaba da shari'ar wadanda suka aikata laifin na Majdanek. A cikin shari'ar farko da aka yi a Lublin a shekara ta 1944, an gabatar da mutane shida a gaban wata kotun laifuka ta musamman kuma aka yanke musu hukuncin kisa. Amma dai, an dauki shekaru talatin wajen gudanar da sharu'ar da ta shafi kisan kiyashin a Jamus ta Yamma. Daga shekarar 1975 zuwa 1981, masu gadi shida da likitan sansanin da wasu sojoji tara sun gurfana a gaban kuliya a Düsseldorf a daya daga cikin shari'a mafi tsawo kuma mafi rikitarwa.