1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guinea: Shekaru biyar da juyin mulki

September 4, 2026

Shekaru biyar da sojoji suka hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Guinea Alpha Condé karkashin jagorancin shugaban kasar na yanzu Mamadi Doumbouya, tun daga wannan lokaci abubuwa da yawa sun faru.

Guinea |Shugaban Kasa | Mamadi Doumbouya Guinea
Shugaban kasar Guinea da ya jagoranci juyin mulki a 2021 Mamadi DoumbouyaHoto: BRENDAN MCDERMID/REUTERS

A ranar biyar ga watan Satumbar 2026 ne, ake cika shekaru biyar da kifar da gwamnatin ta shugaban dimukuradiyya Alpha Condé. A Conakry babban birnin kasar, magoya bayan gwamnati da masu fafutuka na farar hula na da ra'ayi dabam-dabam kan yadda ake tafiyar da kasar. Shugaba Mamadi Doumbouya ya hau karagar mulkin kasar ta Guinea, bayan jagorantar juyin mulkin a shekara ta 2021.

Alkawarin da ba a cika ba

Bayan darewarsa kan madafun iko, ya yi alkawarin gudanar da gajeren zango na rikon kwarya da kuma barin ofis ba tare da tsayawa takara a kowane zabe ba. Sai dai da tafiya ta yi tafiya shugaban ya kai kansa matsayin janar daga na kanar da yake a baya, bayan dandana dadin mulki. An rantsar da Shugaba Mamadi Doumbouya a matsayin sabon shugaban kasa a ranar 17 ga watan Janairun 2026, bayan da ya yi nasarar samun sama da kaso 86 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Disambar 2025. Zaben ya gudana 'yan watanni, bayan amincewa da sabon kundin tsarin mulkin kasar da ya ba shi damar tsayawa takara.

Zaben shugaban kasa a Guenea ConakryHoto: Patrick Meinhardt/AFP

Alseyni Sékou Bangoura shi ne ya yi wa shugaba Mamadi Doumbouya daraktan yakin neman zabe, a yanki na musamman na Conakry a lokacin zaben. Ya kuma bayyana cewa, dimukuradiyya ta zauna a Guinea a halin yanzu. A fagen siyasar kasar an samu wasu sababbin sauye-sauye cikin shekaru biyar da suka gabata, wadanda da alama wasu na ganin sun saba wa ka'idojin dimukuradiyya. Tsohuwar gwamnatin rikon kwarya ta mulkin soja da ta gabata da kuma gwamnati mai ci yanzu, dukkansu karkashin jagorancin Doumbouya sun jefa 'yanci da walwalar al'ummar kasar cikin halin rashin tabbas a cewar dan fafutukar farar hula a Guinea Ibrahima Balaya Diallo.

Sabani da al'ummomin kasa da kasa

Kabinet Fofana manazarcin siyasa ne da ya ce, a fannin diflomasiyya Guinea ta yi nasarar ci gaba da kasancewa a cikin rudani tare da abokan huldar kasa da kasa sabanin wasu kasashen yankin Sahel da suka fito fili da Faransa da ta kasance mai mulkin mallaka. To amma a lokaci guda akwai dan kusanci da Faransa, tun da muradin Faransa ya kasance mai mahimmanci da ya bambanta da na kasashe kamar Nijar da Mali da Burkina Faso.

Fassara: Yacouba Oumarou Maigizawa

Gyarawa da awallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW