Shekaru biyar na kalmar "za mu iya"
September 3, 2020Talla
AN dai bayyamna wannan kalma ta "za mu iya," ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a matsayin kalmar da ta taka muhimmiyar rawa wajen rarraba kawunan 'yan kasar, dangane da batun 'yan gudun hijira.
A shekara ta 2015 ne dai, Merkel din ta furta wannan kalma, kalmar kuma da aka ce ta yi matukar tasiri wajen kwararar miliyoyin 'yan gudun hijira cikin kasar mafi yawansu daga Siriya.
Kalmar "za mu iya" dai, ta kasance kalma mafi tasiri a iya tsawon shekarun da Angela Merkel ta kwashe kan shugabancin gwamnatin Jamus.