1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shekaru biyu da Faransa ta fice a Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB
December 22, 2025

An cika shekaru biyu da ficewar sojojin Faransa daga Jamhuriyar Nijar sakamakon sabanin da kasashen suka samu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar, inda dakarun Faransa ke aikin taimakon tsaro.

Sojojin Faransa lokacin da suke aiki a yankin Sahel na Afirka
Sojojin Faransa lokacin da suke aiki a yankin Sahel na AfirkaHoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

An cika shekaru biyu da ficewar sojojin Faransa daga Jamhuriyar Nijar bayan dauki ba dadi da aka fuskanta na dogon lokaci tsakanin sabin hukumomi na mulkin sojan kasar ta Nijar, da kasar ta Faransa da a wancan lokaci ta ce sam ba za ta taba yarda da wadannan sojoji a matsayin shugabanin kasar ta Nijar ba, wanda kusan har yanzu ake ganin kura ta kasa lafawa tsakanin bangarorin.

Musabbabin takun saka

Sojojin Faransa lokacin da suke ficewa daga Jamhuriyar NijarHoto: Sam Mednick/AP Photo/picture alliance

A ranar 22 ga wata Disamba na 2023 rukunin sojojin Faransa na karshe suka kamala ficewa daga kasar Jamhuriyar Nijar bayan shafe tsawon lokaci ana kai ruwa rana tsakanin hukumomi Nijar na mulkin soja.

Sai dai kuma shekaru biyu bayan ficewar sojojin na Faransa da ma zaman tsama da ake ci gaba da yi tsakanin kasashen biyu wanda al'umma ke ba da ra'ayoyi mabambamta kan tasirin korar sojojin na Faqsansa ko akasin haka.

Sai dai a fannin masu sharhi kan harkokin tsaro da siyasar kasa da kasa irinsu dan jarida Seidik Abba, na ganin cewa shekaru biyu idan aka duba ficewar sojojin Faransa daga kasar Nijar, Faransa ce ta fi hasara ganin yadda kafin nan an koreta daga Mali da Burkina Faso sannan kuma Chadi da Senegal ba su maraba da ita.

Tilas a samu hanyoyin hulda

MAsu zanga-zangar adawa da sojojin Faransa a Jamhuriyar NijarHoto: AFP

Hulda dai tsakanin kasa da kasa idan hara kwai mutunci da gani kima babu zamba cikin aminci, hulda ce da kowa wace kasa ke bukata wanda ita kanta Nijar duk da cewa wannan lamari a tsakaninta da Faransa ya haifar da cece-kuce mai yawa, a cewar Kassoum Issa da a baya ya jagoranci kungiyar kwadago ta ma'aikata, na ganin shi ci gaba sai da hulda tsakanin kasashe domin babu kasar da ta ishi kanta.

A halin yanzu dai za a iya cewa bayan shekaru biyu da korar sojojin Faransa a Nijar har yanzu danganta na ci gaba da tsami tsakanin Nijar din da Faransa inda magabatan a Nijar ke zargin magabatan Faransa da kasa yarda da cewa abin da ya kamata su yi shi ne na mayar da wukakensu kube domin su tunkara wadannan kasashe a matsayin kasashe masu 'yancin kansu ba wai neman ci gaba da hulda irin mai gida da mai bara ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani