Yuganda: Shekaru biyu na hukunta masu auren jinsi
May 14, 2025
Matakin wasu iyaye matan na goya wa 'ya'yansa da ke auren jinsi baya, ya zama banbara-kwai. A Yuganda dai duk wanda ya bayyana kansa a matsayin dan luwadi ko madigo, zai iya fuskantar hukunci. Mama Joseph tana daga cikin wadannan iyaye, ta shaida wa wakilin DW a Yuganda cewa danta bai taba barin kasar ba. Al'umma dai na cewa, dabi'un auren jinsi ba na Afirka ba ne. A takaice dai kalaman Mama Joseph na kalubalantar wannan tunanin da ake da shi, na cewa luwadi da madigo dabi'u ne da suka fito daga kasashen yamma.
Wannan matsaya tata ta jan yo barazana ga rayuwarta daga al'ummar gari da galibi ba su amince da wannan fahimtatat ba, amma duk da haka ta ci gaba da kafewa kai da fata kan matsayarta ta kare danta mai harkar ta LGBTQ. A wasu gidaje a Yuganda, labarai makamantan haka na ci gaba da faruwa. Mama Arthur wata uwa, ta bayyana nata tausayin ga yaronta. Ta shaida wa DW cewa, idan yaro ya fayyace matsayarsa game da auren jinsi ba abu ne mai sauki ba sai dai tana kokarin jan dan nata a jiki. Gwamnatin Yuganda ta ci gaba da kasancewa mai tsauri a kan maganar masu luwadi da madigo, shugaba Yoweri Museveni ya sanya hannu a kan dokar Anti-Homosexuality a shekarar 2023 da ta sa aka kame mutane masu yawa.