Shigar Turquia a Ƙungiyar EU ?
June 13, 2006Tun jiya litinin a ka fara tantanawa tsakanin EU, da ƙasashen Turquia da Crotia, wanda su ka ajje takara.
Bayan wata, da watani, na taƙƙadama a dalili da adawar Sypros, ministocin wajen EU, sun fara tantanawa, a game da matakin farko, daga jerin matakai 35 na karɓar Turquia a sahun ƙasashen EU.
Komishinan EU mai kula da faɗaɗa wannan ƙungiyar ya ce fara tannawa da Turquia ,na matsayin wani babban ci gaba, na dangata tsakin ɓangarorin 2.
Saidai a wani sashen kuma, ministocin harakokin wajen EU, sun rattaba hannu a kann wani daftari, mai kira ga hukumomin Ankara, da su ƙara inganta hulɗoɗi tsakanin su da ƙasar Syprus, da ta zama member a EU, a shekara da ta gabata.
A ɓangaren ƙasar Ƙroshia, ƙasahen EU, na kauttata zaton ba a za a samu wata doguwar matsala ba, idan a ka kwatanta da Turquia.