1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shimfida bututun Gas daga Afirka zuwa Turai

July 29, 2022

Manyan kasashen Afirka masu arzikin mai da suka da Algeria da Najeriya da Jamhuriyar NIjar sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya ta manufa domin aikin shimfida bututun gas zuwa nahiyar Turai.

Mosambik | Provinz Inhambane | Sasol Erdgasexploration
Hoto: Roberto Paquete/DW

Bututun wanda aka yiwa lakabi da Trans-Saharan Gas Pipeline a turance zai kai tsawon kilomita 4, 128 daga Najeriya a yammacin Afirka zuwa Nijar sannan ya dangana da Algeria.

Daga nan bututun zai tunkuda man ta tekun Bahar Maliya zuwa kasar Italiya ko kuma a dauka a tankokin mai zuwa sauran kasasashen Turai.

A lokacin da aka fara gabatar da shawarar gina bututun an kiyasta zai ci tsabar kudi dala Biliyan 10.

nahiyar turai dai na fatan samun makamashin daga Afirka domin rage dogaro akan kasar Rasha.