Shimfida layin dogo daga Cotonou zuwa Yamai
April 7, 2018Shugaba Patrice Talon na kasar Benin da takwaransa Mahamadou Issoufou na Nijar ne suka bayyana wannan aniya tasu ga manema labarai a lokacin wata ziyarar aiki da shugaban kasar ta Benin ya kai Nijar.
Tun a shekara ta 2008 ne dai kasashen Nijar da Benin suka kaddamar da aikin shimfida layin dogo na tsahon kilomita dubu a tsakanin manyan biranen kasashen biyu, amma aikin ya fuskanci cikas a sakamakon rikicin shari'ar da ya hada kamfanin Petrolin na Samuel Dossou da kuma kamfanin Bolore na kasar Faransa kan mallakar wannan kwangila.
Sai dai a watan Oktoba na shekara ta 2017 da ta gabata, wata kotun kasar ta Benin ta halatta wa kamfanin Petrolin wannan kwangila, da ke a matsayin kaso daya daga cikin uku na aikin gina kilomita dubu uku na hanyar jirgin kasa wacce za ta hade kasashen Cote d'Ivoire da Burkina Faso da Nijar da Benin da kuma Togo, da aka fi sani da sunan "Boucle ferroviaire Ouest Africaine"