Shimon Peres ya fara samun sauki
September 15, 2016Talla
Guda daga cikin likitocin wato Rafi Walden ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar tsohon shugaban na iya motsa kafarsa da hannu to amma har yanzu da taimakon na'ura ya ke iya numfashi kuma ba ya iya yin magana. Firamininistan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya ziyarce shi a asibiti a jiya Laraba ya ce al'ummar kasar sun ji dadin labarin da aka samu na alamun saukin da Mr. Peres ya ke nunawa.