1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hatsarin fadin alkarkacin baki a Ghana

February 28, 2022

'Yan jarida da masu fafatuka na kungiyoyin farar hula da ke bayyana ra'ayinsu game da shugabanni da kuma gwamnati na yawan gurfana gaban kotu a kasar Ghana. Ana nuna damuwa da wannan halin da ake ciki.

Shugaba Nana Akufo-Addo na Ghana
'Yan jarida da dama sun fuskanci doka saboda sukar lamirin Shugaba Akufo-AddoHoto: Francis Kokoroko/REUTERS

A kasar Ghana tun daga shekarar da ta gabata kimanin 'yan jarida uku aka kama da wani da ya yi fice wajen rubutu a kafofin sada zumunta na zamani na intanet. Lamarin da tuni ya tayar da hankali a kasar da ke yankin yammacin Afirka da ta yi fice wajen 'yancin fadin albarkacin baki.

Kundin tsarin mulkin kasar ta Ghana na shekarar 1992 ya ba da 'yancin fadin albarkacin baki, amma 'yancin na cikin tasku. A watan Febrairu 'yan sanda sun tuhumi Kwabena Bobie Ansah mai gabatar da shirye-shirye a gidan rediyon Accra FM da laifin yada labaran karya bayan da ya ce matar shugaban kasar Rebecca Akufo-Addo tana amfani da damfara wajen karbe filayen gwamnati domin amfani da su bisa kashin kai. Kuma ana ci gaba da shari'ar.

Kana an ci tarar wani mai sharhi a kafofin yada labarai tara kan raina kotu, bayan zargin Shugaba Nana Akufu-Addo na kasar ta Ghana da hada baki da alkalai kan shari'ar zaben shekara ta 2020.

Kamun ludayen gwamnati ya dauki hankali yanzu inda 'yan Ghana da yawa ke gangami karkashin taken #FixTheCountryHoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images

Kwamitin kare 'yan jarida na duniya na cikin wadanda suka nuna damuwa kan abin da ke faruwa a kasar. Alhassan Suhuyini tsohon dan jarida kana dan majalisar dokoki ya ce yanayin da ake ciki akwai damuwa sosai.

"'Yan jarida da dama sun fuskanci tsangwama a wani bangare daga jami'an gwamnati. Akwai abin da ya saka aka soke dokar hukunta rubutun da suka saba muradun wani, inda hakan ya kasance daya daga cikin abin da shi kansa shugaban kasar yake tunkaho ya taka rawa wajen kawo karshen aiki da dokar."

Karin bayani: An kama mai shirya juyin mulki a Ghana

Shi dai Shugaba Nana Akufo-Addo na cikin gwagwarmayar neman soke dokar tauye fadin albarkacin baki lokacin da yake dan gwagwarmaya, amma yanzu ana ganin ya sha bamban da abin da shi kansa ya yi imani da shi.

Aikin jarida a Ghana ya bunkasa sakamakon tanade-tanaden kundin tsarin mulkin 1992Hoto: GEORGE OSODI/AP Photo/picture alliance

Alexander Afenyo Markin dan majalisar dokoki na bangaren jam'iyya mai mulki ya musanta cewa gwamnatin tana yarfe ga masu caccakarta ko neman tauye 'yancin fadin albarkacin baki tare da neman 'yan jarida su yi taka tsantsan lokacin da suke aiki.

"Muna da masu rubuce-rubuce da yawa a shafukan sada zumunta na zamani na intanet, inda ake samun rashin nunaq zahirin abin da ke faruwa, haka ya dace ya zama abin da duk muke nuna damuwa a kai. Ya dace mu ba su goyon bayan da ya kamata, a rahoto tare da rubuta labarai, amma da su kula da duk bangarorin da abin ya shafa bisa hanyoyin da ya dace ya kasance."

Karin bayani: Ghana: Zanga zangar matasa kan gyaran kasa

Sai dai a cewar lauya Kofi Bentil duk wanda ya samu madafun iko yana nuna wuce gona da iri:

"Akwai abin da za a ce kashin bayan siyasa kuma irin wannan kashin bayan, ya shafi duk gwamnatocin, abin da za ka gani. Ina tsammani abokanmu da suke kan madafun iko ya dace su nuna damuwa da wannan hali. Ya kasance yanayin da mutum zai yi rubutu da zaran ka karanta ka fahimta sai ka saka a kama shi, ana kama 'yan jarida ta ko'ina."

'Yan jarida da kungiyoyin fararen hula na kasar ta Ghana na ci gaba da nuna damuwa da yanayin.