1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana iya shirya sahihin zabe a Najeriya?

May 7, 2026

Shugaban hukumar zabe ta kasar Farfesa Josh Amupitan dai ya shaidwa babban sufeton 'yan sandan Najeriya cewa zai yi wuya a iya samun ingantacce kuma sahihin zabe a sassa daban-daban da ke cikin kasar saboda rashin tsaro.

Hukumar azben Najeriya
Hukumar azben NajeriyaHoto: Patrick Meinhardt/AFP

Akwai damuwa bisa makomar zaben Najeriya na shekarar badi ta 2027, inda shugaban hukumar zabe ta kasar Farfesa Josh Amupitan ya ce da kamar wuya hukumar ta INEC ta kai ga ingantaccen zabe cikin yanayin rashin tsaron da ke a Najeriya yanzu haka.

To sai dai kuma Amupitan daga duk alamu ya tayar da hankali na masu adawa ta kasar da ke fadin a kai ga kasuwa tunanin jibge sojoji a lokutan yin zabe. Duk da karuwar rashin tsaron dai masu adawa na zargin kokarin tsorata masu zabe na kasar kan hanya ta magudin zabukan.

Matsalolin tsaro suna iya rikita zabe

Hukumar zaben NajeriyaHoto: Patrick Meinhardt/AFP

Kama daga kasuwa harkokin noma dai sannu a hankali rashin tsaron da ke Najeriya na tasiri a rayuwa da makoma ta 'yan kasar a halin yanzu. To sai dai kuma babbar barazana daga duk na alamu na zaman tasirinsa a kokarin samar da shugabannin kasar a shekarar badi.

Shugaban hukumar zabe ta kasar Farfesa Josh Amupitan dai ya shaidwa babban sufeton 'yan sandan Najeriya cewar fa da kamar wuya iya samun ingantacce kuma sahihin zabe a sassa daban-daban da ke cikin kasar, ba tare da nazarin yanayin tsaron da ke a Najeriya a halin yanzu ba.

A zabukan can baya dai sai da ta kai ga Abuja dage zabuka sakamakon barazanar rashin tsaron a sassa da yawa.

Sa'insa tsakanin 'yan adawa da masu mulki

Jami'an tsaron NajeriyaHoto: Nuhu Gwamna/REUTERS

To sai dai kuma yanzu daga duk alamu kalaman INEC na neman jawo dagun hakarkari cikin gida na masu adawar Najeriya da ke masa kallon da biyu.

Ladan Salihu dai na zaman kakaki cikin gidan ADC ta adawar da ke cewa daukacin rashin tsaron da ke daukar hankali a Najeriya a halin yanzu dai na faruwa ne a sashen arewacin kasar. Sashen kuma da masu adawa ke kallon wurin samun kuri'a a kokarin cika buri.

A cewar hukumar jami'an tsaron da ke a Najeriyar ke da babban aikin tsare rumfunan yin zaben, INEC din a tunanin kabiru Adamu da ke sharhi cikin rashin tsaron na da rawar takawa a kokarin kyautata lamura.

APC ta amince Tinubu ya yi takara

Shugaba Tinubu ya sayi fom na takara a zaben 2027

47:33

This browser does not support the video element.

Ko a cikin wannan mako dai APC mai mulki ta ce, Shugaba Bola Tinubu bai bukatar tantance shi kan hanyar takara a zaben na badi.

Bala Ibrahim dai na zaman daraktan labaran jam'iyyar da kuma ya ce Tinubu ya riga ya yi ta maza cikin batun mulkin kasar.

Nigeria dai na dada nisa kan hanyarkai wa zuwa ga zabukan cikin hayaniyar da ke da girman gaske a shekara mai zuwa ta 2027.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani