1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na neman sake kulla hulda da Nijar

Gazali Abdou Tasawa AH
September 6, 2024

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta sanar da amincewa da tayin da Amirka ta yi mata na bude sabon babin hulda a tsakanin,amma ban da katsalandan.

Niger | U.S. und nigerianische Flagge vor Luftwaffenstützpunkt in Agadez | 2018
Hoto: Carley Petesch/AP Photo/picture alliance

 A wani sharhi da gidan talabijin na gwamnatin kasar ta Nijar ya gabatar kan ganawar wakilan gwamnatin Amirka da na Nijar ba tare da sanya miryoyin bangarorin ba , ya bayyana cewa  da yake jawabi a gaban tawagar Amirkawan ministan cikin gida na Nijar Janar Mohamed Toumba ya fara da nuna rashin jin dadinsa dangane da yadda ya ce Amirka ta yi gum da bakinta tana kallon Faransa a loakcin da ta nemi cuta wa Nijar.  ta hanyar amfani da kungiyar CEDEAO. Dangane da tayin Amirkar na bude sabon babin hulda da Nijar, ministan ya ce a shirye Nijar take ta amince da hakan amma a bisa wasu sharudda na ganin Amirka ta shafa wa Nijar Lafiya wajen zaben kasashen da ta  ga dama ta yi hulda da su a duniya.

Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Ministan ya ci gaba da gayawa jami'an gwamnatin ta Amirka cewa duk wata hulda da wata kasa ke nema da Nijar a nan gaba za ta mayar da hankali ne ga kare muraden Nijar da tabbatar da cikakken ‚yancinta. Kuma duk kasar da ba ta mutunta haka ba, to kuwa nan take  Nijar za ta katse hulda da ita. Da yake tsokaci kan wannan batu, Farfesa Sani Roufa'i  mai sharhi kan harkokin tsaro a Nijar ya ce akwai darasi a cikin abin da ke faruwa tsakanin kasashen biyu.

Ali Mahamane Lamine Zeine firaministan NijarHoto: Balima Boureima/Anadolu Agency/picture alliance

''Abin mamaki ne a ce kasar da tsawon shekaru ake dauka a matsayin ta karshe a duniya, amma ta zo take fadin irin wadannan kalamai a gaban manyan kasashe kamar Amirka. Lallae za a iya cewa a yau duniya ta sauya. Kuma irin wadannan kalamai da minista ya fada a gaban 'yan Amirka. Ba wata kasa ce za ta zo ta ce mata ga wadanda za ta yi hulda da su ba. To amma ka ga su Amirkawa da yake suna tafiya da yadda duniya ta sauya da kuma kare muradensu, ba su yi irin na Faransaba, sai suka zo suka amince a tafi da su.''

Hoto: ISSIFOU DJIBO/EPA

Sai dai kungiyar Debout Niger ta bakin shugabanta Malam Ismael Mouhamadou ta ce akwai bukatar hukumomin mulkin sojan Nijar su yi taka tsan-tsan da wannan tayi sulhu na Amirka. ''Akwai lauje cikin nadi dan haka ya kamata gwamnatin Nijar ta yi taka tsan-tsan. Saboda mun san tarihin Amirka mun san makircinsu da duk abin da suka tubka wa kasashe wadanda suka juya masu baya. Saboda yau Nijar na hulda da Rasha da wasu kasashe irin su Iran wadanda ba sa ga maciji da ita, dan haka muna tsoron kar a je wani zagon kasa ne take son shirya wa Nijar .'' To amma wasu masu adawa da mulkin sojan Nijar na ganin tayin da Amirkar ta yi wani hannunka mai sanda ne ga hukumomin mulkin  sojan kasar. 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani