Taron AU da EU: Akwai riba ga Afirka?
November 24, 2025
Tun bayan taron karshe da aka yi a Al-Kahira a shekarar 2000, shugabannin nahiyoyin biyu da dama ke halartar wannan taron, wanda a wannan ke zuwa a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 25 da kulla kawancen EU da AU. Taron hadin gwiwar karo na bakwai tsakanin kungiyar Tarayyar Afirka da ta Tarayyar Turan ya zo a wani muhimmin lokaci ga nahiyoyi biyu, sakamakon tasirin da wasu manyan kasashe ke samu a nahiyar Afirka kamar China da Rasha da Turkiyya da Indiya.
Babbar abokiyar cinikayya
Wannan ne dalilin da ya sa kungiyar Tarayyar Turan, ke neman ci gaba da habaka kawancenta da kasashen Afirka. Hasali ma dai, Hukumar Zartaswa ta kungiyar Tarayyar Turan ta bayyana cewar, EU na ci gaba da kasancewa abokiyar cinikayya ta fako ga nahiyar Afirka, ma'ana tana gaban Chaina da Indiya da Amurka.
Sannan Brussels ta kara cewa, kimanin kashi 90% na kayayyakin da ake fitarwa daga Afirka suke shiga kasuwar Turai da ta kunshi al'umma miliyan 450 ba tare da biyan haraji ba, sakamakon yarjejeniyoyi da suka shafi kasashe 19 a nahiyar Afirka. Bayan taron kolin karshe da ya gudana a Brussels a shekarar 2022, shugabannin Afirka da Turai suna tattauna muhimman batutuwa guda biyu, ciki har da hanyoyin karfafa hadin gwiwa a fannoni kamar zaman lafiya da tsaro da shugabanci na gari da na 'yan gudun hijira.
Mabambantan Ra'ayoyi
Sai dai kuma ana samun sabanin ra'ayoyi a kan wadannan batutuwa, a tsakanin nahiyoyin biyu. Shugabanni Turai da Afirka na amfani da wannan dama wajen duba manufofin Ci-gaba mai Dorewa da Majalisar Dinkin Duniya ta gindaya, kuma ake neman cimma kafin nan da shekara ta 2063, wadanda suka yi daidai da manufar hadin gwiwa tsakanin AU da EU na 2030.
Shugaban Hukumar Zatarwa na kungiyar Tarayyar Afirka, dan kasar Djibouti Mahmoud Ali Youssouf na daga cikin mahalarta wannan taro na koli, baya ga Félix Tshisekedishugaban kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da kuma Emmanuel Macron shugaban kasar Faransa, wanda ya fara rangadin wasu kasashen Afirka tun a karshen makon da ya gabata, kuma zai kammala da Afirka ta Kudu.