1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SHIN WAI DA AKWAI BUKATAR SHIRYA ZABEN RABA GARDAMA KAN KUNDIN TSARIN MULKIN KASASHEN EU A NAN JAMUS KUWA ?

YAHAYA AHMEDApril 23, 2004

Tun da Frimaiya Tony Blair na Birtaniya ya ba da sanarwar shirya zaben raba gardama, don tabbatad da amincewar `yan kasarsa ko kuma yin watsinsu da sabon kundin tsarin mulkin Kungiyar Hadin Kan Turai ne, wasu bangarori suka fara kururuwan gudanad da irirn wannan zaben a nan Jamus. Jam’iyyun adawa ne dai ke jagorancin wannan salon. To amma, wai shin Jamus na bukatar gudanad da zaben raba gardama kan wannan batun kuwa a zahiri ?

Valéry Giscard d'Estaing da Firamiyan Italiya Silvio Berlusconi, suna gabatad da daftarin kundin tsarin mulkin Kungiyar EU
Valéry Giscard d'Estaing da Firamiyan Italiya Silvio Berlusconi, suna gabatad da daftarin kundin tsarin mulkin Kungiyar EUHoto: European Commission Audiovisual Library

Duk wadanda suka rungumi tafarkin dimukradiyya da hannu biyu-biyu dai, za su yi amanna da kiran da jam’iyyun adawa ke yi na shirya zaben raba gardama a nan Jamus, kwatankwacin wanda Firamiyan Birtaniya Tony Blair, ya ba da sanarwar za a yi a kasarsa, don warware rikcin da ake yi kan cancantar samad da wani sabon kundin tsarin mulki na bai daya, ga kasashen kungiyar Hadin Kan Turai.

Magoya bayan manufar kafa hadaddiyar kasa ta nahiyar Turai kuwa, suna dari-dari da irin wannan shawarar. Saboda, idan mafi yawan jama’a suka jefa kuri’un na ki a zaben raba gardamar, to duk wasu kafofin kungiyar Hadin Kan Turan, za su rasa muhimmancinsu kuma ke nan. Idan aka yi la’akari da wasu matakan da aka dauka can baya, za a iya ganin cewa, mafi yawan al’umman kasashen nahiyar ba su amince da shigo da kudin Euro, ko kuma fadada kungiyar zuwa gabashin Turai ba.

A nan Jamus ma, mutane da dama ne ke nuna rashin sha’awarsu ga al’amuran da suka shafi harkokin siyasar kungiyar. Wasu kuma sun ce, ba su da cikakken bayani game da ababan da ke wakana a cibiyoyin kungiyar. Har ila yau dai, wasu kuma na ganin cewa, babu wata moriyar da Jamus ke ci a matsayinta na `yar kungiyar.

Kawo yanzu dai, jami’an siyasa ne ke yan ke duk wasu shawarwari game da harkokin kungiyar. A galibi kuma, suna yanke shawarar ne duk da rashin amincewar mafi yawan al’umman nahiyar. A lal misali, mafi yawan Jamusawa ne suka nuna matukar adawarsu ga shigo da sabon kudin nan na Euro don ya maye gurbin Deutsch-Mark. Amma duk da hakan, sai da jami’an siyasar suka ci gaba da manufarsu tare da yin zaton cewa, idan aka shigo da kudin, ko ta yaya dai ai jama’a za su amince da shi.

Duk da sukar da mabiya tafarkin dimukradiyya ke yi wa salon rashin neman ra’ayin jama’a kafin yanke muhimman shawarwari, da kungiyar Hadin Kan Turai ke bi, akwai dai wasu fa’idoji kuma, da salon ke janyowa.

Babbar nasarar da kungiyar ta cim ma a tarihinta dai, ita ce shawo kan rikice-rikice a nahiyar, wadanda a da suke ta janyo barkewar yake-yake.

Amma abin da masharhanta ke ta tambaya a nan Jamus shi ne, ko mene ne ya sa jam’iyyun adawa ke ta nacin sai an shirya zaben raba gardama a kan sabon kundin tsarin mulki na kasashen kungiyar ? A lokacin da suke jan ragamar mulki, su ne masu matukar adawa ga duk wata kira ta shirya irin wannan zaben. A zahiri dai, dabararsu ita ce, suna son yin amfani da zabukan ne wajen matsa wa abokan hamayyarsu lamba. Ashe ko ba abin mamaki ba ne, yin watsi da jam’iyyun gwamnati na SPD da Greens, suka yi da wannan kiran.

Abin da ake bukata a nan Jamus dai shi ne, yin cikakkiyar muhawara kan ababan da ke kunshe cikin sabon kundin tsarin mulkin, don jama’a su fadaka da su. Daga bisani ne kuma, za a iya neman jin ra’ayin al’umma, kafin a tsai da shawarar shirya zaben raba gardama.

Amma muddin jama’a ba su san ma ko me ake ciki ba, to duk wani zaben raba gardamar da za a shirya, ba zai amfanad da kowa ba, sai masu kururuwar neman yin hakan ne kawai za su cim ma gurinsu, wanda kuma ba lalle ba ne ya dace da na al’umman kasa baki daya.