1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barcelona ta yi kaca-kaca da Real Madrid

Mouhamadou Awal Balarabe SB
October 28, 2024

Dukan kawo wuka da Barcelona ta yi wa Real Madid ya jawo wa Lamine Yamal da Alejandro Balde kalaman wariyar launin fata.

Sifaniya | El Clasico | wasan Real Madrid da FC Barcelona
'Yan wasan BacelonaHoto: Alberto Gardin/NurPhoto/picture alliance

Gasar nahiyar Afirka ta kwallon kafa a bakin teku ta kammala a Hurghada da ke kasar Masar bisa sabuwar nasarar Senegal da ke neman zama gagarabadau a wannan fanni. Zakuna na Teranga za su ci gaba da rike kambunsu bayan da suka doke Moritaniya da ci 6-1 a wasan karshe. Wannan shi ne karo na takwas da kasar Senegal ta lashe kofin kwallon kafa na bakin teku, kuma karo na biyar a jere. Baya ga Moritaniya a matsayi na biyu, ita kuwa Moroko ta haye matsayi na uku bayan da a wasan neman matsayi ta doke Masar mai masaukin baki da ci 4-3.

Karin Bayani: Labarin Wasanni: Bayern ta yi kunnen doki

Patrice Motsepe shugaban hukumar kwallon kafa ta AfirkaHoto: BackpagePix/empics/picture alliance

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka Patrice Motsepe, ya yi amfani da wannan dama wajen nuna jin dadinsa kan yadda ake samu bunkasar Kwallon bakin teku a akasarin kasashen wannan nahiya. Sannan ya jaddada mahimmancin inganta gasar kwallon kafa ta bakin teku a sauran kasashen Afirka da ba su rungumi wasan ba, don ya kama mizanin beach soccer na duniya. A shekara mai zuwa kuma a karon farko, wata kasa ta Afirka wato Seychelles za ta karbi bakuncin gasar cin kofin kwallon bakin teku ta duniya a watan Mayu 2025.

Hukumar Tseren Keke ta Duniya ta janye tseren Tour du Faso da ke gudana yanzu haka a Burkina Faso daga jadawalinta, saboda shigar da tawagar kasar Rasha da masu shirya gasar suka yi. Dama dai a fili yake cewar dokokin UCI sun haramta wa 'yan tseren Rasha shiga duk gasannin da ke karkashin kulawarta tun bayan da ta mamaye Ukraine, fiye da shekaru biyu da rabi da suka gabata. Sai dai mahukunta Burkina Faso sun yi buris da wannan matsaya, inda suka gayyaci 'yan tseren CSKA Moscow,  a tseren da ke zama na 35 da suka shirya.

Burkina Faso tseren kekeHoto: AP

Wannan haramci na iya haifar da mummunan sakamako ga tseren keke a Burkina Faso, Ssaboda matakan ladabtarwa da za su iya biyo baya, duk da tutiyar da take yi da wannan gasa a nahiyar Afirka. Tseren Tour du Faso  ya sha fama da matsalar tsaro a kasar a shekarun baya-bayan nan, lamarin da ya kai ga soke tseren a 2022. Amma daga bisani, tseren ya ci gaba da wanzuwa bisa kula daga Hukumar Tseren Keke ta Duniya UCI, wanda ke da mahimmanci wajen samun karbuwa.

Yanzu kuma sai mufi nahiyar Turai, inda duk hankula suka karkata ga karon batta da ya gudana tsakanin Real Madrid da FC Barcelona a babban lig na kasar Spain. Sai dai sabanin yadda aka saba gani a shekarun baya-bayannan, 'yan wasan Barcelona ne suka mamaye kuma suka murkushe 'yan Madrid a gida da ci 4-0, lamarin da ya kawo karshen caffin da 'yan Madrid ke yi na haduwa goma duka goma, kuma ya ba wa Barcelona damar ja wa Real Madrid birki a jerin wasanni 40 da ta yi ba tare da shan duka ba.

'Yan wasan BacelonaHoto: Guillermo Martinez/NurPhoto/picture alliance

Sai dai 'yan wasan Barcelona Lamine Yamal da Alejandro Baldé sun fuskanci wariyar launin fata daga magoya bayan Real Madrid lokacin da suke murnar nasarar mai cike da tarihi. Amma dai kungiyar Real Madrid ta fitar da sanarwa inda ta yi Allah wadai da cin mutuncin da wasu magoya bayanta, kuma ta ba da tabbacin gudana da bincike don gano wadannan suka watsa faifain bidiyo na munanan kalamai da nufin daukar matakan ladabtarwa da na shari'a a kansu. Ita ma ministar shari'a da kula da hijira

 Elma Saiz, ta goyi bayan Lamine Yamal, inda ta ce "Ba za mu kyale wariyar launin fara ta samu gurbi a fannin wasanni ba."

A sauran manyan lig na nahiyar Turai, wasu manyan kungiyoyi sun yi karon batta, inda a gasar Premier League ga misali, Arsenal da Liverpool sun tashi ci 2-2, kuma wannan ya bai wa Manchester City damar dawowa a saman teburi. A Italiya kuwa, an yi kunnen doki 4-4 tsakanin Inter Milan da Juventus. Sai dai Napoli da ta doke Lecce da ci 1-0, ta kara yi wa masu biya mata bayya zarra. A Faransa kuwa, Paris Saint Germain ta gasa wa Olympique de Maseilles aya a hannu da ci 3-0, a wasan Classico, lamarin da ya bai wa kungiyar babban birnin faransa dawowa a saman teburin Ligue 1.

A nan gida Jamus, bayan kammala mako na takwas na gasar Bundesliga, Bayern Munich ce ke kan gaba da maki 20 bayan da ta yi wa Bochum da ke zama 'yar baya ga dangi, dukan kawo wuka ci 5-0. Vincent Kompany da ke zama kocin Bayern, ya yaba da kwazon 'yan wasansa, musamman ma dangane da ruwan kwallaye da suka yi.

"Ina ganin cewar wasa ne mai kyau, cikakke kuma babu kuskure. Mun zura kwallaye biyar, amma ya kamata mu zura fiye da haka, muna matukar farin ciki da yadda wasan ya gudana, mun ci kwallaye tara wasanni biyu, don haka abu ne mai kyau. "

Bochum da Bayern Munich a gasar BundesligaHoto: INA FASSBENDER/AFP

Duk da cewa Bayern ce ke a matsayi na farko, amma har yanzu tana tafiya kafada da kafada a yawan maki da RB Leipzig, wacce ita ma ke da maki 20 bayan da ta samu nasara a kan Freiborg da ci 3-1. Sai da Amadou Haidara da takwarorinsa suka zagen dantse tujuna Laipzig ta kai bantenta, sakamakon mamaye su da Freiburg ta yi kafin a tafu hutun abin lokaci. Ita kuwa, Bayer Leverkusen ta yi amfani da rashin nasara na Freiburg wajen dawowa matsayi na uku bayan da ta tashi 2-2 da Werder Bremen. Wannan dai shi ne kunnen doki na uku da Leverkusen ta yi tun bayan fara kakar wasan bana.

Xabi Alonso da ke horas da Bayer Leverkusen ya ce 'yan wasansansu ba su nuna kwazo sosai ba.

"Ba mu samu zarafin nuna juriya, da kalubalantar abokan hamayya da samun natsuwa da muke bukata a lokacin da muke kan gaba ba. Ina ganin cewar, ko a farkon rabin lokaci, ba mu nuna karfin hali a cikin 'yan mintunan karshe, lokacin da suka zura kwallo ta biyu ba. Ya kamata ya zama darasi a gare mu, mu koyi rashin ba da kai da wuri, dole ne mu kare kanmu cikin azama."

A sakamakon sauran wasanni mako na takwas na Bundesliga kuwa, Borussia Dortmund ta sake yin abin fallasa, inda ta sha duka a hannun Augsburg da ci 2-1, lamarin da ya jefa Yaya-karama cikin wani sabon rikici. Hasali na, Wasan da Dortmund za ta yi da Wolfsburg a gasar kalubale na neman cin kofin kwallon kafar Jamus na wannan makon ka iya zama mai yanke hukunci kan makomar Nuri Sahin a matsayi mai horas da BvB. A nata bangaren, Stuttgart ta doke Holstein Kiel da ci 2-1, yayin da aka yi kunnen doki 1-1 tsakanin Mainz da Borussia Monchengladbach. Ita kuwa 'yar auta St Pauli ta yi canjaras da Wolfsburg.

Ballon D'OrHoto: picture-alliance/abaca

A Wannan Litinin ne a birnin Paris na kasar Faransa, ake gudanar da bikin bayar da Ballon d'Or karo na 68, kyautar da ake bai wa gwarzon dan wasan kwallon kafa da ya fi nuna bajinta a duniya a shekara. A rukunin mata, 'yar Spain Aitana Bonmati da ke bugawa a Barcelona na daga cikin wadanda ake kyautata wa zato, ko da shi ke 'yan mata Afirka biyu na iya ba da mamaki ciki har da Tabitha Chawinga, 'yar wasan Malawi da ke taka leda a Olympique Lyonnais. A bangaren maza kuwa, dan wasan da ya lashe gasar zakarun Turai da gasar La Liga ta SPain a karkashin Real Madrid, Vinicius Jr, shi ne babban wanda aka fi kyautata wa zato saboda rashin tabuka abin kirki daga Kylian Mbappé da Erling Haaland. Amma dai Rodri, wanda ya lashe gasar Euro a karkashin Spain na iya zame wa Vinicius babban kalubale. Sannan dan wasa daya ne Ademola Lookman na Najeriya da ke bugawa a Atalanta Bergmane zai wakilci Afirka a bana, sakamakon zura kwallaye uku da ya yi a wasan karshe na cin kofin Europa a karawa da Bayer Leverkusen.