1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko hakkin dan Adam zai samu kariya?

Salissou Boukari LMJ
December 10, 2025

Jamhuriyar Nijar kaman sauran kasashen duniya, ta bi sahu wajen tunawa da ranar hakkin dan Adam da ake bikin tunatawa a duk ranar 10 ga watan Nuwamba na kowa ce shekara.

Majalisar Dinkin Duniya | Ranar Kare Hakkin dan Adam | Nijar
Majalisar Dinkin Duniya kan ware ranaku domin tunawa da wasu muhimman batutuwaHoto: Alexander7/Zoonar/picture alliance

Wannan batu na kare hakin dan Adam batu ne da a kullum kowa ke yi, amma kuma akasari wajen aiwatarwa ana shan bam-bam. A wata hira da ya yi da DW, Malami a jami'ar birnin Tahoua Dakta Atto Namaiwa na ganin cewa, lallai wasu lokutan ana samu kura-kurai wajen kare hakkin dan Adam din da ya kamata a gayara.

Rana mai muhimmanci

Wannan rana ta tunawa da kare hakkin dan Adam, wata dama ce ta nunawa a fili cewa kowa na da alaka da kare hakkin dan Adam da ke zaman tamkar tsara rayuwar al'umma ta yau da kullum.

Lauya mai fafutuka wajen kawar da rashin adalci a Yuganda

01:41

This browser does not support the video element.

A wannan lokaci na tashin hankali da rashin tabbas da mutane da yawa ke jin karuwar rashin tsaro, da rashin yarda da kuma kawar da kai kan wasu abubuwan da ya kamata a duba.

'Yancin dan Adam a Nijar

Taken ranar kare hakkin dan Adam din ta bana, na nufin sake tabbatar da kimar 'yancin dan Adam da kuma nuna cewa sun kasance masu karfi ga dan Adam. A bangaren gwamnatin Nijar ofishin ministan shari'a musamman sashen daraktan mai kula da kare hakin dan Adam, sun dukufa wajen ganin an bayar da karfi a fannin hadin kan al'umma da cudanya da juna cikin mutuntawa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani