1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shinfida bututun mai daga Nijar zuwa Najeriya

Abdoulaye Mamane Amadou GAT
February 1, 2018

Nijar da Najeriya sun cimma yarjejeniyar shinfida bututun mai daga Agadem zuwa Kaduna tare da gina matatar mai ta hadin gwiwa a cikin daya daga cijin jihohin Najeriya na kan iyaka da Nijar.

Turkmenistan Gasförderung
Hoto: picture alliance/dpa/ChinaFotoPress


Gwamnatocin kasashen Nijar da Najeriya sun kulla wata yarjejeniya da ke shirin shimfida bututun danyen mai daga Nijar zuwa Najeriya tare da kafa matatar mai ta zamani a daya daga cikin jihohin Najeriya da ke makwaftaka da Nijar. Ministocin harkokin albarkatun mai na kasashen biyu ne suka bayyana hakan a kasashen a wata ziyarar aiki ta wuni daya da ministan harkokin albarkatun man Tarayyar Najeriya ya kawo a wannan mako a Nijar.

Hoto: picture alliance/dpa/ChinaFotoPress

Yarjejeniyar da kasashen biyu da suka cimma a ranar Laraba 31 ga wannan watan Janerun 2018, ta samo tushe ne tun a shekaru biyun da suka gabata inda Nijar ta nuna sha’awarta ta fitar da danyen mai zuwa matatar man fetur ta Kaduna da ke Tarayyar Najeriya bayan shimfida bututun danyen a nisan kilomita sama da dubu daga garin Agadem Arewa maso gabascin kasar zuwa Kaduna. Sai dai bisa wasu manyan dalilai masu nasaba da rashin samun daidaito na nau'in danyen man da Nijar ke hakowa zuwa matatar man ta kaduna, hukumomin kasashen biyu sun dakatar da batun kana kuma suka ci gaba da nazari da tattauanwa kan batu har ya zuwa wannan lokaci da suka cimma matsaya a kai. Babban burin da sabon tsarin yake son cimma shi ne na kawo masalaha tsakanin al’ummomin kasashen Inji ministan albarkatun man fetur din Tarayyar Najeriya Dr Emmaneul IBE:
 
"Daga farko dai don a samu ingantacciyar hulda ne tsakanin Najeriya da Nijar, idan an yi wannan zai baiwa Nijar damar fitar da danyen mai, kenan an samu sasaukar hanyar da za a kai man a waje kuma hakan ba zai tsaya nan ba zai baiwa kasashen biyu damar samun cigaban al’ummarsu tare da baiwa matasa ayyuka da haifar da ciniki da kuma bunkasa kasashen yammacin Afirka"
 
Allah ya albarkanci jamhuriyar Nijar da dimbin danyen man fetur wanda ya kai ta ga shiga tsara tun a 2011. Sai dai kuma ganga dubu 100  ce kawai ta man kasar ke haka a wuni a karkashin yarjejeniyar da ta hada ta da wani kamfanin hadin gwiwa tsakanin China da Nijar wato CNPC wanda ke daukar kashi 80 cikin dari na man kana ya baiwa kasar ta Nijar kaso 20 cikin dari, wanda shi kansa ya fi karfin wanda kasar ke amfani da shi a wuni. A don haka ta ke son sayar da wani kaso a kasashen makofta irin su Najeriya.

Ministan mai na kasar Nijar Foumakoye GadoHoto: DW/A. M. Amadou

Kana kasashen biyu na Nijar da Najeriya dai sun kuma cimma yarjejeniyar samar da wata sabuwar matata a daya daga cikin jihohin Najeriya da ke makwaftaka da Nijar don taimaka wa Nijar cin moriyar arzikinta. Malam Foumakoye Gado shi ne ministan albarkatun man fetur na kasar Nijar:

"Wannan matakin ya zo ne a cikin yanayin da muka jima muna tattauanwa na ganin Nijar ta fitar da danyen manta a waje daga farko kamar yanda kuka sani mun kudri anniyar garzayawa zuwa matatar mai ta Kaduna sai dai bisa wasu dalilai muka fasa. To amma daga baya mun samu fasahar gina wata matatar mai sabuwa tsakanin iyakokin kasashen biyu don tace danyen man da za mu fitar zuwa kasuwannin duniya. Kuma saboda wannan batun ne takwarana ministan albarkatun mai na Najeriya ya zo a nan Nijar don karkare wannan batu"

Ministan mai na Najeriya Dan EteteHoto: picture-alliance/dpa/G. Barbara

Tuni kasashen biyu suka ambaci daukar matakin kafa kwamitin na musamman da zai kai ga daddage maganar tare da tantance adadin gangar man da ma hanyoyin shimfidar bututun man za ta shafa daga mahakar man Nijar ta Agadem da ke Diffa zuwa kan iyakar ta Tarayyar Najeriya. Kuma tuni masanan tattalin arziki da masu sharhi a kasar kamar su Malam Siradjo Issaka suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu:

"Man fetur din Nijar bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta shi da na Najeriya. Kenan abin alfahari ne idan an samu taimakon kasa kamar Najeriya wajen bunkasa harkar man fetur zai taimaka sosai".

Tun a shekarun 2013 ne gwamnatin ta Nijer ke da sha’awar fitar da danyen manta wanda daga farko ta ambaci kai shi a gabar KIRIBI ta Kamaru bayan ya bi ta kasar Tchadi lamarin da ya sha fuskantar suka da kuma kalubalai barkatai. Wannan matakin na Nijar da Najeriya na zuwa ne a yayin da kasashen biyu ke cikin tsananin bukata wa lau ta man fetur ga Najeriya da yanzu hakan ke cikin wani mawuyacin hali, a yayin da ita kuwa Jamhuriyar ta Nijar ke cikin tsanain buktar kudi na rarar ma’adanai duba da yanda matsin tattalin arziki ke addabarta kana bai wuce kaso 5 cikin dari ba kurum da arzikin ma’adanunta na karkashin kasa ke samarwa.