Shinzo Abe ya gana da Donald Trump
November 18, 2016![USA Japan Abe Trump Treffen](https://static.dw.com/image/36432325_800.webp)
Talla
Wannan ganawa ta biyo bayan irin kalaman da Mr Trump ya yi amfani da su lokacin yakin neman zabe da ake ganin akwai yuwuwar Amirka ta janye dakaru a kasashen da take da hulda ta kut-da-kut kamar Japan.
Bayan ganawar ta sa'a guda da rabi tsakanin shugaban mai jiran gado na Amirka Donald Trump, da Firaminista Shinzo Abe na Japan, a birnin New York, babu cikakkun bayanai kan batutuwa da mutanen biyu suka tattauna a kai.