Nijar: Rayuwar mata dalibai a jami'a
August 19, 2019Talla
A kasashen Afirka musamman ma a yankuna da Hausawa ke da yawa, akwai muhawara mai karfin gaske da ake yi kan yanayi na tarbiyya ta dalibai mata da ke karatu a jami'a. Wasu dai na yi musu kallon mutanen kawai yayin da su daliban mata kan ce ba haka lamarin yake ba domin galibinsu karatunsu suke yi jami'a kamar takwarorinsu maza ba wai yawon banza ne ya kai su ba. Shirin ya duba yadda lamarin yake a Jamhuriyar Nijar.