Shirin Abu Namu
October 8, 2018Talla
Yayin da ake ci-gaba da yaki da wannan dabi'a dai, wasu kungiyoyi masu fafutuka a arewacin Najeriya sun ce sun sake bankado wani sabon salo da ake amfani da shi wajen bautar da mata da yaran mata da kuma matsalar yawaitar yi wa yara kanana fyade. A wannan karon matsalar aikatau ta kunno kai ta kuma yi kaka-gida a tsakanin ma'aurata inda aka gano yadda wasu maza suka yi musayar aikin daukar dawainiyar iyali da ya rataya a wuyansu suka aza wa matansu.
Shirin Abu Namu ya yi kokarin ji daga bakin matan da lamarin ya shafa ba tare da yin nasara ba, amma wata ganau ta bayyana halin da ire-iren matan da ake magana a kansu suka samu kansu na yin aikin aikatau kafin su ciyar da iyali.