Shirin EU kan masu kaucewa biyan haraji
May 22, 2013Shugabanin gwamnatocin tarayyar turai na shirin daukar sabbin matakan yaki da masu kauce wa biyan haraji daya kunshi makuddan kudade, a taron da za su gudanar a wannan larabar a birnin Brussels din kasar Belgium. Sai dai babu alamun shugabannin turan zasu iya shawo kan kasashen Austria da Luxemburgh su amince da wannan a yarjejeniyar da suke muradin cimma a taron nasu. Da karuwar yawan marasa aikin yi da, da matsayin kudin euro da koma bayan tattalin arziki tsakanin kasashen dai, akwai fatan cewar taron na yini guda zai cimma yarjejeniyar da zata yaki masu kaucewa biyan haraji, domin sake farfado da kungiyar. A wasikar daya aike wa shugabannin kungiyar, shugabanta Herman Van Rompuy, ya bayyana shawo kan matsalar masu kauce wa biyan haraji da zambatar gwamnaki a matsayin wata hanya da za ta taimaka wa matsanacin hali da wasu kasashe ke ciki.
Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu