1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaAfirka

Shirin hada rigakafin Covid-19 a Senegal

Suleiman Babayo LJM
June 6, 2021

Senegal da ke yankin yammacin Afirka za ta fara yin maganin rigakafin cutar coronavirus daga shekara mai zuwa karkashin wata yarjejeniya da kamfanin hada magunguna na kasar Belgium.

Senegal Dakar | Pflegepersonal | Pikine Hospital
Hoto: Getty Images/AFP/J. Wessels

Akwai yuwuwar kasar Senegal da ke yankin yammacin Afirka za ta fara yin maganin rigakafin cutar coronavirus daga shekara mai zuwa karkashin wata yarjejeniya da kamfanin hada magunguna na kasar Belgium Univercells domin bunkasa shirin samar da rigakafin cutar a nahiyar Afirka.

Wata majiya wadda ke cikin masu samar da kudin ta tabbatar da wannan labarin ga kamfanin dillancin labaran Reutrs. KAsashe masu arziki sun fara bude kafar samar da rigakafin bayan sun fara samu, nahiyar Afirka tana sahun baya wajen samar da rigakafin cutar. Nahiyar mai mutane kimanin milyan dubu-da-300, sai dai mutane milyan 7 kacal aka yi wa cikekken alllurar rigakafin cutar ta coronavirus.

Matakin kamfanin na Univercells na fara samar hada maganin rigakafin a kasar Senegal zai karfafa samar da fadada yawan masu samun rigakafin a yammacin Afirka da dama Afirka baki daya.