Najeriya: An karfafa tsaro a jihar Kano
April 14, 2023Rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta ce, ta tanadi jami'an tsrao sama da dubu biyar don gudanar da aikin da kuma magance barazanar ‘yan daba lokacin kammala zabukan da ba su kammala ba a ranar Asabar mai zuwa. Yan kwanakin nan, ayyukan ‘yan daba ya zama babbar barazana ga al'ummar jihar Kano lamarin da ke tsoratar da mutane wajen fita wannan zabe, Hukumar zabe ta INEC dai ta ce, ta kammala nata shirye shiryen.
A Asabar din nan ne za'a kammala zabukan da suka gamu da tazgaro a babban zaben da ya gabata a sassan Najeriya daban daban. A jihar Kano, Hukumar zabe ta ce, ta kammala nata shirin na tabbatar da zaben ya kammala cikin kwanciyar hankali sai dai mutane na fargabar yadda zaben zai kasance, la'akari da yadda a ‘yan kwanakin nan ayyukan 'yan daba ya ke ta karuwa.
To amma guda daga cikin ‘yan siyasa Ahmed Aruwa ya soki lamirin cewar sune ke bai wa matasan kwaya, yana mai cewar daga gida suke zuwa a jangale, sai dai guda daga cikin wakilan kungiyoyin kishin al'umma, Hajiya Halima Ben Umar ta musanta wannan batu inda ta ce, hakika 'yan siyasa ne kanwa uwar gamin bai wa matasa kwayoyi.
Ambasada Abdu Abdullahi Zango kwamishinan zabe a Kano, ya bayyana cewar za'a gudanar da zaben ‘yan majalisu ne a kananan hukumomi 14, sai kuma na ‘yan majalisun tarayya guda biyu wato Fagge da Tudun Wada da Doguwa. Yanzu haka jami'yyu sun ja daga suna jiran lokaci domin zaben Kano yana da muhimmanci wajen samun rinjaye a majalisar dokokin jihar.