1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar PDP ta kammala yakin neman zabe

February 20, 2023

Bangarori daban-daban na fitowa don nuna dan takarar da suke goyon baya a yayin da aka kammala shirin gudanar da babban zaben Najeriya.

Zaben Najeriya na 2023
Zaben Najeriya na 2023Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Kasa da mako guda da kai wa ya zuwa babban zabe, hankali na masu siyasar tarrayar Najeriya na kara karkata ya zuwa goyon baya na masu ruwa da tsaki da harkoki na kasar da ke kara yawa cikin fagen siyasa ta kasar.

Kama daga shugaban kasar ya zuwa ga malaman addinai, ko bayan kungiyoyin kare muradu na kabilu da ma uwa uba kananan jam'iyyu, sha'awa na kara fitowa fili da kila tunanin in da yawu na 'yan kasar ke shiri ya karkata a yayin zabe.

Mutum sama da miliyan 93 suka yi rijistar zabeHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP

Kuma tun daga karshen mako dai, maita na kara bayyana cikin kasar in da kusan kowa ke kara fitowa fili tare da nuna gwaninsa cikin fagen da ke da tsirin gaske. Shi kansa shugaban kasar alal ga misali bai boye goyon baya na Ahmed Bola Tinubu da ke neman dorawa bisa jagoranci na masu tsintsiyar.

Can ma tsakanin manya na kungiyoyin al'adu ra'ayi yana rabe a tsakanin Ohaneze ta 'yan kabila ta Igbo da ke goyon bayan Peter Obi da 'yan uwansu na Afenifere na kabilar Yarbawan da ke fadin ko Tinubu ko kafar katako.

Peter Obi da Bola Tinubu da kuma Atiku Abubakar Hoto: K. Gänsler/DW, Shengolpixs/IMAGO, EKPEI/AFP

To sai dai kuma sashen arewacin tarrayar Najeriyar na shirin taka rawa yayin zaben ba tare da wani dan takara na goyon baya ba. Akalla biyu a cikin 'yan takara guda hudu da ke sahun gaba dai sun fito a arewacin yankin.

A cikin al'ada, batun na goyon baya ya dade cikin fage na siyasar tarrayar Najeriya inda batun addini da kabila da kila ma muradin son rai, kan rinjayi tunani zuwa ga goyon baya ga masu takarar. Kuma ko baya na kungiyoyin sa kai, ya zuwa yanzun, akalla jam'iyyu kusan bakwai sun janye a takarar tare da nunin goyon baya ga manya na masu takarar guda hudu.

A ranar Talata mai zuwa, ake saran kammala yakin neman zaben jam'iyyar APC mai mulki a yayin da yar uwarta ta PDP ta kare nata a karshen mako.