1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Talaka zai amfana da shirin inshorar lafiya

Zulaiha Abubakar
September 23, 2018

Firaministan Indiya Narendra Modi ya kaddamar da wani shirin inshorar lafiya wanda zai agaza wa sama da mutane miliyan 500 marasa karfi a kasar.

Indien | Patient mit durch Smog verursachten Atemnotproblemen
Hoto: Getty Images/AFP/M. Sharma

Ana sa ran jihohin kasar 29 za su dinga zuba gudummawar kudin da yawan su yakai Dalar Amirka biliyan daya da rabi a kowacce shekara don taimakawa marasa lafiyan da basu da karfin neman magani.

Indiya dai na fama da yawaitar marasa lafiya bayan karancin likitoci a asibitocin gwamnati da kasar ke cigaba da fuskanta yayin da asibitoci masu zaman kansu ke tsawwala kudin ganin likita da na magani.